Daga JOHN D. WADA a LAFIYA
A cigaba da bikin makon tunawa da muhimmancin shayar da jarirai nonon uwa da ake gudanarwa a ƙasar nan da duniya bakiɗaya na shekarar 2024, Shugabar Jami’ar Jihar Nasarawa da ke garin Keffi, Farfesa Sa’adatu Hassan Liman ta yi kira na musamman ga iyaye bakiɗaya musamman waɗanda ke tasowa su tabbatar suna shayar da jariran su nonon uwa idan aka yi la’akari da muhimmancin haka ga rayuwan jariran nasu dama su iyayen kansu.
Farfesa Sa’adatu Hassan Liman ta yi wannan kira na musamman ne a lokacin da ta ke zanta da manema labarai dangane da muhimmancin makon shayar da jarirai nonon uwa na bana a ofishinta da ke babbar jami’ar ta gwamnatin jihar a makon da ya gabata,
Ta ce, ba shakka kiran ya zame wajibi don a yanzu binciken fannin lafiya ya bayyana muhimmanci da wasu ingantattun sinadare da ke cikin nonon uwa waɗanda jarirai ke matuƙar buƙata a yanzu haka da suke tasowa.
Farfesa Sa’adatu Hassan Liman ta ƙara da cewa bayan wadannan amfani da nonon mama ke yi wa rayuwa da lafiyar jariran yana kuma haɗa kyakkyawar zumunci da dangantaka tsakani uwa da ƙan nata akoyaushe sabodahaka acewar ta ya zama wajibi wa iyayen su tabbatar suna yin la’akari da hakan.
Ta yaba wa fannin kiwon lafiya na duniya baki ɗaya dangane da hangan nesa da a cewar ta suka yi na kebe makon a kowanne shekara don tunawa da ranar dake da manufar jawo hankulan iyaye mata musamman wadanda ke haihuwa a yanzu na su fahimci mahimmancin shawar da jariran nasu inda ta buƙaci a cigaba da gudanar da ire-iren bukukuwan.
Shugabar jami’ar ta gwamnatin jihar Nasarawa farfesa Sa’adatu Hassan Liman ta kuma yi amfani da damar inda ta yaba wa gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule dangane da ƙirƙiro tareda aiwatar da wasu kyawawa kuma ingantaccen shirye-shirye da dama da a yanzu hake suke cigaba da inganta harkokin mata da lafiyar su da na ’ya’yan su baki daya inda ta buƙaci sauran gwamnonin ƙasar nan da masu hannu da shuni baki ɗaya suyi koyi da gwamna Sule musamman ta zuba jari a hukumomin inganta lafiyar iyaye mata da ’ya’yan su don kasancewa idan iyaye basu samu isheshen lafiya da kulawa ba to ba shakka al’umma baki ɗaya hakan zai shafe su.
A hanzu haka dai binciken wakilin mu ya gano cewa ana cigaba da gudanar da wasu muhimman bukukuwan makon na shayar da jarirai nonon mama a jihar ta Nasarawa da Nijeriya dama duniya baki ɗaya wato na shekarar 2024 da ake ciki kenan kamar yadda aka saba yi a kowanne shekara.
