Miyetti Allah ta yi Allah-wadai da kisan da aka yi wa Sarkin Gobir

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah ta yi Allah-wadai da sace-sacen mutane da azabtarwa da kuma kisan gilla da aka yi wa Sarkin Gobir na Gatawa a ƙaramar Hukumar Sabon Jihar Sakkwato, Alhaji Isa Bawa.

Sakataren ƙungiyar ta MACBAN na ƙasa, Malam Bello Aliyu-Gotomo ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Aliyu-Gotomo ya ce, kisan da aka yi wa basaraken ba wai kawai ya tayar da hankali ba ne, illa dai yana nuni da irin ta’asar da masu aikata ta’addancin suka aikata.

A cewarsa, babu hujjar ayyukan waɗannan ƙungiyoyin masu kisan kai.

“MACBAN ta jajantawa Gwamnatin Jihar Sakkwato, Sarkin Musulmi, da iyalan Sarkin da aka kashe da kuma ɗaukacin al’ummar Jihar.

“Muna kira da babbar murya ga Gwamnatin Tarayya da ta kara ƙaimi wajen yaƙi da ‘yan bindiga da garkuwa da mutane da ke addabar wasu jihohin Arewa maso Yamma.

“MACBAN ta nisanta kanta daga wannan aiki da kuma duk wani nau’i na laifi da kowace ƙungiya ta aikata domin ba ta wakiltar laifi ko masu laifi.

“An ba da izinin aikata laifuka a waɗannan yankunan ya yi ta’azzara na dogon lokaci yana mai wahala ga ayyukan yau da kullun na mutanen da ke zaune a can.”

Ya kuma yi kira ga daukacin jihohin yankin Arewa maso Yamma da su sake tunanin dabarunsu na magance matsalar rashin tsaro da ya raba miliyoyin mutanen karkara daga gidajensu.

Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya ya ruwaito, Aliyu-Gotomo ya ce, “A madadin ɗaukacin mambobinmu da ke faɗin ƙasar nan, muna yi wa Sarkin Gobir addu’ar Allah ya ba Sarkin Gobir lafiya, ya kuma sa Aljannar Firdausi ta zama masaukinsa na ƙarshe.

“Allah Ta’ala Ya baiwa iyalai aarfin gwiwar jure wannan babban rashi.

“Muna addu’a da fatan za a tona asirin waɗanda suka aikata laifin nan take kuma a yi musu hukunci mai tsauri.”

By ukarofi