Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da kasancewa cikin ƙungiyar ’yan fashin teku a jihar Bayelsa, yayin da suke kammala shirinsu na sace wani jirgin ruwa ɗauke da ɗanyen mai a yankin Tekun Guinea.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa an cafke mutanen ne a wani otel da ke Titin Tenacious a unguwar Edepie da ke Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.
An bayyana sunayensu da Geoffrey Atizara mai shekaru 38 daga Aleibiri a ƙaramar hukumar Ekeremor ta jihar Bayelsa, da kuma Divine Kelechi Unueze mai shekaru 42 daga Nekede a Owerri, jihar Imo.
Rahotanni sun nuna cewa binciken farko da aka gudanar, wanda ya haɗa da bayanan sirri da kuma amincewar da wadanda ake zargin suka yi, ya nuna cewa su da wasu mambobin ƙungiyarsu suna shirin kwace wani jirgin ruwa, su sace ma’aikatansa tare da kwasar kayan da yake ɗauke da su.
Wata majiya ta ce Unueze ne ke ɗaukar nauyin kudi na shirin, yayin da Atizara ke da alhakin nemo ƙarin mutanen da za su shiga aikin fashin tekun. Majiyar ta ƙara da cewa, su biyun sun amsa cewa suna cikin wata babbar aungiyar masu aikata laifuka da ke aiki a yankunan Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu na Nijeriya, inda suka fi samun riba ta hanyar fashin teku da kuma satar mutane.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa, idan aka yi la’akari da yadda ƙungiyar ke da kayan aiki da dabaru na zamani, kamun nasu ya daƙile babbar barazana da ka iya shafar tsaron zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin Tekun Guinea, wanda ke da matukar muhimmanci ga harkokin man fetur.
Wata majiya ta daban ta ce DSS na aiki kafaɗa da kafaɗa da Rundunar Sojin Ruwa ta Nijeriya da sauran hukumomin tsaro domin ƙarfafa ayyukan tattara bayanan sirri da nufin dakile matsalolin tsaro a tekun.
Ta ce a baya-bayan nan an samu nasarar tare wasu kwale-kwalen ’yan fashin teku tare da kuɓutar da ma’aikatan wasu jiragen ruwa da aka sace a gabar tekun jihohin Bayelsa da Delta.
An kuma bayyana cewa wannan nasara na daga cikin jerin matakan da hukumomin tsaro ke ɗauka domin tabbatar da zaman lafiya a yankin, musamman ma a hanyoyin sufurin ruwa masu alaka da harkokin man fetur. A cewar majiyoyin, hakan na kara tabbatar da aniyar hukumomi na rage ayyukan ta’addanci da ke shafar tattalin arziki da tsaron ƙasa.
