Ba mu san abin da aka amince da shi a sabbin dokokin haraji ba – Makinde

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana damuwa kan yadda aka tafiyar da sabbin dokokin haraji a Nijeriya, yana mai cewa har yanzu gwamnonin jihohi da ma jama’a ba su san takamaiman abin da Majalisar Tarayya ta amince da shi ko abin da aka rattaba wa hannu ya zama doka ba.

Makinde ya bayyana hakan ne yayin wani taron jama’a inda ya ke jawabi ga tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo.

A jawabinsa, gwamnan ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda Osinbajo ya bar muƙami, yana mai cewa tsarin shugabanci na tattaunawa da sauraron juna da ya saba gani a wancan lokaci ya ragu a yanzu.

Ya tuna da wani muhimmin taron Majalisar Tattalin Arzikin ƙasa (NEC) a farkon shekarar 2020, lokacin ɓarkewar cutar COVID-19, inda aka tattauna batun killace ƙasar baki ɗaya. A cewarsa, taron ya kasance mai zafi, amma Osinbajo, wanda ke jagorantar zaman a lokacin, ya bai wa kowa damar faɗar ra’ayinsa ba tare da tilas ba.

Makinde ya ce, salon jagorancin ne ya bai wa jihohi damar saukar matakan da suka dace da yanayin yankunansu, yana mai nuni da cewa dalilin da ya sa bai kulle jihar Oyo gaba ɗaya a wancan lokaci ba shi ne saboda an bai wa gwamnoni damar yin hukunci bisa la’akari da halin da jama’arsu ke ciki.

Sai dai ya ce akasin hakan ne ya faru game da sabuwar dokar haraji. A cewarsa, gwamnoni sun nemi a dakatar da ƙudirin domin a sake dubawa cikin natsuwa, amma ƙorafe-ƙorafensu ba su samu kulawar da ta dace ba.

Makinde ya ce, “Mun ce a dawo da ƙudirin harajin domin mu zauna mu duba shi ba tare da son rai ba. Amma abin da muka gani shi ne rashin haƙuri da sabanin ra’ayi.” Ya ƙara da cewa a halin yanzu akwai ruɗani kan ainihin sigar dokar da aka amince da ita.

Batun dokokin harajin ya janyo cece-kuce a faɗin ƙasar, inda wasu gwamnatocin jihohi, ƙungiyoyin farar hula da masana tattalin arziki ke nuna damuwa kan yadda aka gaggauta amincewa da su ba tare da cikakkiyar tattaunawa ba. Wasu na ganin hakan na iya shafar tsarin tarayya da yadda ake rabon kuɗaɗen shiga tsakanin matakan gwamnati.

Rahotanni daga Majalisar Wakilai ma sun nuna cewa ana zargin an samu wasu sauye-sauye ba bisa ƙa’ida ba a cikin dokokin da aka wallafa a jaridar gwamnati, saɓanin abin da ‘yan majalisa suka amince da shi tun farko. Wannan zargi ya kara jefa batun cikin duhu, tare da kara kira ga a fito da cikakken bayani domin kawar da shakku a zukatan jama’a.

Masu lura da al’amuran siyasa na ganin cewa batun haraji ba ƙaramin abu ba ne a tafiyar da mulki, domin yana da nasaba kai tsaye da rayuwar jama’a da kuma ikon jihohi a tsarin tarayya. Saboda haka, suna jaddada buƙatar gaskiya da buɗe ƙofa ga tattaunawa domin dawo da yarda tsakanin gwamnati da al’umma.

By ukarofi