Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD
Farashin mai ya ɗan ƙaru a kasuwar duniya a makon da ya gabata, inda alamun tashin hankali na siyasa, sauye-sauyen kasuwanci daga Amurka da ƙaruwar buƙatar mai daga ƙasar Chana suka ƙara ɗaure kasuwar.
A ƙarshen mako, ɗanyen mai na Brent, ma’aunin farashin mai na duniy, ya tashi zuwa kusan dala 64.41 kowace ganga, ƙaruwa ta kusan kashi 1.3 idan aka kwatanta da makon da ya gabata. West Teɗas Intermediate (WTI) na Amurka ma ya yi ƙasa da ƙasa ya kai dala 60.31 kowace ganga, yana daidai da ƙaruwa ta kimanin kashi 1.8% a makon nan.
Masana kasuwa sun ce farashin ya sami goyon baya ne bayan rahotanni da suka nuna cewa shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya dakatar da wasu shirye-shirye na kai hari kan Iran — abu da ya rage tsoron samun matsaloli wajen fitar da mai daga yankin Gabas ta Tsakiya. Sai dai har yanzu yanayin siyasa ya kasance mai tayar da hankali, musamman da ake ci gaba da sa ido kan batutuwan kasuwanci da takunkumi a kan ƙƙsashen Venezuela da Iran, waɗanda dukkaninsu na taka muhimmiyar rawa a kasuwar mai ta duniya.
Haka kuma bayanan tattalin arzikin China, wanda ya nuna ƙaruwar buƙatar kayayyaki da ƙarfin tattalin arziki, sun ƙara ƙarfafa tsammanin cewa buƙatar mai za ta kasance mai ƙarfi, duk da raɗaɗin da wasu ke yi kan tattalin arzikin duniya.
Wannan ne ya sa farashin ya sami ɗan ɗagawa, duk da cewa akwai damuwa kan manufofin kuɗi da tasirin manyan kasuwanni.
Duk da wannan ƙaruwar farashin a makon nan, ƙwararru a fannin suna jaddada cewa kasuwar mai na fuskantar damuwa da abubuwa da dama — ciki har da tsare-tsaren samar da mai na ƙasashe da lamuran siyasa — duk waɗanda ke iya canja yanayin farashi cikin sauri a makonni masu zuwa.
