Dubun wani tsohon soja mai yi wa Boko Haram safarar makamai ta cika a Bauchi

Daga BASHIR ISAH

Rundunar Sojin Nijeriya ta bayyana cewar, jami’anta sun kama wani tsohon soja da ake zargi da yi wa Boko Haram safarar makamai a Jihar Bauchi.

Cikin bayanan da ta fitar a ranar Juma’a, rundunar ta ce, “A ranar 18 ga Yuli, 23, jami’anta sun cafke wani da ake zargi mai safarar makamai ne a Boi cikin yankin Ƙaramar Hukumar Bogoro a Jihar Bauchi.

“Binciken farko ya gano wanda ake zargin korarren soja ne a Damasak. Askarawa sun gano ƙananan bindiga 2, bindiga ƙirar magazine 2 da kuma alburusai,” in ji rundunar.

Kazalika, rundunar ta ce ta sake kama wasu mutum biyu da ake zargin masu taimaka wa mayaƙan Boko Haram ne a kasuwar Kukareta da ke Ƙaramar Hukumar Damaturu, Jihar Yobe, inga suka ƙwace wayoyi da kuɗi da sauransu daga hannunsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *