Gwamna Lawan ya karrama mahajjaciyar da ta mayar da tsuntuwar Dala 80,000 a Saudiyya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawan, a ranar Alhamis, ya karrama hajiyar da ta mayar wa mwanda ya jefar da Dala 80,000 a wajen aikin Hajjin da ya gabata a ƙasar Saudiyya.

Mahajjaciyar, Hajiya Aishatu ‘yar Guru Nahuce daga Ƙaramar Hukumar Bungudu ta jihar Zamfara ta tsinci Dala 80,000 (N64,240,000) sannan ta miƙa su ga jami’in hukumar jin daɗin alhazai ta Zamfara domin mayar wa ga mai shi.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta ce gwamnan ya karrama mahajjaciyar ne tare da dukkan sarakunan jihar, wanda ya gudana a zauren majalisar da ke gidan gwamnati.

Gwamnan ya kuma bayyana matuqar farin ciki da gwamnatin jihar ta nuna kan sahihancin hajiyar.

“Dukkan al’ummar jihar Zamfara suna alfahari da farin ciki kan abin da Hajiya A’ishatu ta yi a Saudiyya, ya ƙara wa ɗaukacin al’ummar Zamfara suna.

“Abin alfahari ne a gare mu Hajiya A’isha, an rubuta sunanta a cikin litattafan tarihi masu kyau, irin wannan abin ana so ne ga duk wani Musulmi mai aminci, musamman a ƙasa mai tsarki.

“Mun ga misali ƙarara na gaskiya da ya kamata a yi koyi da Hajiya A’isha, ki yarda, ba kowa ne zai iya samun irin waɗannan maƙudan kuɗaɗe a wurin da ba kowa, ya mayar da su.

“Gwamnatin jihar Zamfara za ta yi duk mai yiwuwa don taimakawa iyalan Hajiya Aisha.

“Shugaba Bola Ahmed Tinubu kuma zai karrama Hajiya A’isha bisa wannan aiki na gaskiya.”

Tun da farko, Sarkin Bungudu, Alhaji Hassan Attahiru yayin gabatar da Hajiya A’isha, ya jaddada cewa matakin da ta ɗauka ya ƙara mutunta al’ummar Zamfara baki ɗaya.

Hajiya Aisha ta kuma bayyana yadda lamarin ya faru a ƙasa mai tsarki ta Saudiyya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *