Hukumar CAC ta yi taron wayar da kan hukumomin tsaro da masu kamfanoni a Kano

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Hukumar Yi wa Kamfanoni Rijista ta Ƙasa ta yi taro na wayar da kan jami’an tsaro, hukumomi masu yaƙi da cin hanci da rashawa da sauran ƙungiyoyi masu zaman kansu.

Taron wanda aka gudanar a Jihar Kano ya samu halartar shugaban hukumar ta ƙasa Garba Abubakar da sauran masu ruwa da tsaki na hukumar da ‘yan kasuwa wakiilan jami’an tsaro da ƙungiyoyi.

Da yake zantawa da manema labarai shugaban hukumar ta CAC na ƙasa Garba Abubakar ya ce taron na wayar da kan jami’ai ne da ƙungiyoyi da masu zuba hannun jari da masu gudanar da kamfanoni.

Ya yaba da yadda mutane suka ba su goyon baya suka halarci taron.

Garba ya ce an yi bayanai mahalarta taron su ma sun yi an kuma yi tambayoyi na abinda ake so a san an amsa musu.

Ya ce jami’an tsaro da suke binciken masu laifi na da kyakkyawar rawa da zasu taka wajen gano wanda ya yi al’mundahana ko ya yi amfani da kuɗi wajen bai wa ‘yan ta’adda ko wanda ya kwashi kuɗi ya ɓoye taron zai sauƙaƙa aikin jami’ai za su yi amfani da rijista da suka kawo daga ko’ina ba sai lallai sun nemi bayanai daga hukumar ba, hakan zai taimaka musu wajen aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *