Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
A ƙokarinsa na tallafawa waɗanda hare-haren ‘yan bindiga ya shafa dan majalisar tarayya mai wakiltan ƙananan hukumomin Musawa da Matazu Abdullahi Aliyu Dujiman Katsina ya raba kuɗi da raguna ga al’ummarsa.
Wannan tallafi da ya samar haɗin gwiwa ne da gidauniyar Gwagware da hukumar bada agajin gaggawa ta ƙasa NEMA.
ɗan majalisar ya bayar da kuɗi Naira miliyan 11 da raguna guda 250 da aka rabawa mutane 1,100 Naira dubu goma kowannesu.
Ita kuma gidauniyar Gwagware ta samar da Naira miliyan 30 ga mutane 500 da suka fito daga ƙananan hukumomin Musawa da Matazu.
Kamar yadda mataimaki na musamman kan yaɗa labarai na ɗan majalisar Francis Sardauna ya faɗa wa manema labarai ita hukumar NEMA ta raba wa mutanen da hare-haren ya shafa su 500 kayan masarufi.
Kayan sun haɗa da masara, shinkafa, sutura da sauransu.
A jawabinsa Dujiman Katsina ya tabbatar wa al’ummar yankin cewa zai cigaba da yin duk abinda ya kamata wajen tabbatar da samun dawwamammen zaman lafiya a yankin da jihar Katsina baki ɗaya.
Hon. Abdullahi Aliyu ya ce wannan tallafi da aka raba masu kaɗan ne “ƙarin wasu na nan zuwa bada jimawa ba da yardar Allah, Dujiman ya ce.
Ya yi kira ga al’ummar yankin da su taimakawa gwamnatin jihar da jami’an tsaro wajen samun
dawamammen zaman lafiya a yankin da jihar bakiɗaya.
Da yake jawabi shugaban Gidauniyar Gwagware Alhaji Yusuf Aliyu Musawa ya yaba wa ɗan majalisar kan abubuwan alheri na cigaban yankin da yake kawowa.
ɗan majalisar wanda shugaban kwamitin harkokin cikin gida na Majilisar wakilai shine ya kawo hukumar NEMA da gidauniyar Gwagware domin tallafawa waɗannan mutane su samu su yi hidimar sallah.
