Aminu ‘Yanbiyu ya zama Sarkin Fawan garin Festac a Legas 

Spread the love

Daga DAUDA USMAN a Legas

A ranar Lahadin da ta gabata ne masarautar Mai martaba Sarkin Fulanin Jihar Legas, Dakta Alhaji Abubakar Mohammed Bambado na biyu ta gudanar da taron naɗe-naɗen sarakunan Hausawa na unguwanni daban-daban dake cikin garin Legas.

Taron naɗin sarautun ya samu halartar Sarkin Fawan Jihar ‘egas Alhaji Bala Katako abbatuwa Okoba Agege da Sarakunan fawan Legas da sarakunan Hausawa na unguwarni daban-daban na cikin garin Legas da sauran al’ummar Arewacin Nijeriya mazauna Legas bakiɗaya.

 Haka kuma taron ya gudana ne a harabar fadar mai martaba Sarkin Fulanin na Legas dake unguwar Surulere cikin garin Legas.

A cikin sarakunan da masarautar ta sarkin Fulani ta naɗa a kwai Alhaji Aminu ‘Yam biyu ɗan asalin jihar Jigawa mazaunin garin Festac wanda masarautar ta naɗa shi matsayin sarautar Sarkin Fawan Festac da kewayenta gabaɗaya.

Kafin naɗa Alhaji Aminu ‘Yan biyu sarautar sarkin fawan Festac sai da sakataren fadar Sarkin Fulanin na jihar Legas ya karanto kaɗan daga cikin tarihin Sarkin Fawan inda sakataren ya cigaba da bayyanawa al’umma a wajen taron cewar kafin Alhaji Aminu ‘Yan biyu ya zama sarkin fawan garin Festac ya bada gudummawa maitsoka ta ɓangarori daban-daban a garin Festac a cikin gudummawar da ya da hadda wanzar da zaman lafiya a garin Festac dama jihar legas baki ɗaya sakataren ya ce adun haka yake ganin Alhaji Aminu ‘Ya  biyu ya can canta aba shi wannan sarauta kuma a ganinsa Alhaji Aminu ya zama garkuwar  matasa da sauran dattawan Hausawa mazauna garin Festac da kewayenta gabaɗaya.

Sannan ‘yan majalisun fadar Sarkin Fulanin suka bada dama aka naɗa Alhaji Aminu ‘Yan biyu matsayin sarautar sa ta sarkin fawan garin Festac da kewayenta gaba ɗaya. 

Hakazalika Sarkin Fulanin na jihar Legas ya cigaba da yi wa sababbin sarakunan huɗuba dangane da yanda za su cigaba da jagorancin al’ummarsu a cikin adalci. Ya ce ya kamata sarakunan su ƙara haƙuri kan wanda suke da shi domin samun nasarorin jagorancin al’ummarsu.

Da yake tsokaci dangane da samun sarautar tasa, Sarkin Fawan Festac Alhaji Aminu ‘Yanbiyu ya cigaba da gabatar da godiyarsa ga ‘yan majalisun fadar mai martaba Sarkin Fulanin Legas dangane da cancantarsa da suka gani suka ba shi wannan sarauta. Hakazalika ya ce yana mai gabatar da wata godiyar ga fadar mai martaba sarkin Hausawan Festac Alhaji Mustapha Musa Katsina Jagaban Festac ya ce shi ma yana yi masa fatan alheri dangane da gudummawar da ya bada dangane da naɗa shi wannan sarauta.

A ƙarshe ya ce yana yi wa kowa fatan alheri dangane da wannan al’amari.

By ukarofi