Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana yadda ya tsira daga wani mugun shiri da tsohon Shugaban ƙasa, Janar Sani Abacha, ya kitsa domin kashe shi, bayan da aka kama shi tare da Janar Shehu Musa Yar’Adua da attajirin ɗan kasuwa kuma wanda ya lashe zaɓen Yuni 12 na 1993, Cif MKO Abiola.
Manhaja ta rawaito cewa Obasanjo ya danganta tsira da rayuwarsa da ya yi ga rahamar Ubangiji.
Obasanjo, wanda ya kai ziyara Ogbor Uvuru a Aboh Mbaise, Jihar Imo a ƙarshen makon da ya gabata don ƙaddamar da coci ta Assemblies of God da aka sanya masa suna “The Noah’s Ark” wanda wani mai bayar da gudummawa kuma ɗan kasuwa , Obioma Success Akagburuonye, ya gina kuma ya ba da kyauta, ya bayyana cewa a wancan lokacin, Shugaban ƙasa ya yi ikirarin cewa ba za su fito daga gidan yari da rai ba, domin ya ci gaba da mulki har abada.
Ya ce: “Lokacin da aka kama ni, mutumin da ya kama ni na ɗauka kuskure yake yi. Ya yanke shawarar cewa dole a kawar da wasu daga cikinmu idan har zai ci gaba da riƙe mulki har abada. Na samu kaina a wannan hali, amma da farko na rude, domin ban san laifin da na aikata ba. Shin kuskure ne?”
“Da na fahimci ba kuskure ba ne, na koma ga addu’a, ciki har da irin addu’ar da Istifanos ya yi, amma na sauya ta kadan. Na ce ko suna sane da abin da suke yi ko ba su sani ba, ya Allah ka gafarta musu.”
“Na miƙa kaina ga Allah. Kuma mutumin da ya kama mu ya yi iƙirari cewa ba za mu fito daga da rai ba — cewa MKO Abiola ba zai fito da rai ba, Shehu Yar’Adua ba zai fito da rai ba, da kuma Olusegun Obasanjo ba zai fito da rai ba.
“Daga cikin ukun da ya ce ba za su fito da rai ba, biyu ba su fita da rai ba. Ni ne kaɗai na fito da rai, ba saboda ƙarfina ba, amma saboda rahamar Allah ta musamman.”
