Duniya na jiran Amsa daga “mai iƙirarin kare haƙƙin bil’adama”

Daga CMG HAUSA

A baya-bayan nan, ƙwararru kan kare hakkin dan Adam masu zaman kansu guda 14 na Majalisar Ɗinkin Duniya sun fitar da wata sanarwa ta haɗin gwiwa, inda suka buƙaci gwamnatin Amurka da ta dawo da kadarorin biliyoyin daloli mallakar babban bankin ƙasar Afghanistan.

Biliyoyin daloli za su iya ceton rayuwar al’ummar duk ƙasar Afghanistan. Alƙaluman ƙididdigar da hukumomin ƙasa da ƙasa suka fitar sun nuna cewa, sama da mutane miliyan 23 a Afghanistan na buƙatar agajin abinci cikin gaggawa. Bugu da ƙari, sama da ‘yan Afghanistan miliyan 4 ne suka rasa matsugunansu.

Shin alhakin wane ne? Ko shakka babu Amurka ce. A shekara ta 2001, Amurka ta ƙaddamar da yaki a Afghanistan bisa dalilin wai “yaƙi da ta’addanci”. Yakin na tsawon shekaru 20, ya yi sanadin mutuwar fararen hula ‘yan Afghanistan 100,000, kuma kusan miliyan 11 sun zama ‘yan gudun hijira.

A watan Agustan shekarar da ta gabata, a ƙoƙarin da take yi na daidaita manyan tsare-tsarenta a duniya, Amurka ta yi gaggawar janye sojojinta daga Afghanistan. A watan Fabrairun wannan shekara, shugaban Amurka ya sanya hannu kan wata doka, da nufin raba kusan dala biliyan 7 na kadarorin Babban Bankin Afghanistan da Amurka ta kwace zuwa gida biyu, za a yi amfani da kashi 1 don biyan diyya ga waɗanda suka yi hasara a lamarin ranar 11 ga watan Satumba ko kuma harin “9.11”.

Ban da wannan kuma, a matsayinta na babbar mai haddasa rikicin Ukraine, Amurka ta amince da samar wa Ukraine rukunonin makamai guda takwas, jimillar taimakon soji da ta samar ta kai dalar Amurka biliyan 3.7. Kwace kudi daga Ukraine, raunana Rasha, lalata Turai, wadatar da masana’antun sojinta… Duk wadannan su ne ainihin abin da Amurka take so.

Duniya na jiran Amurka “mai ikirarin kare haƙƙin bil’adama”, ta mayar da martani ga sukar da ƙwararrun kare haƙƙin bil’adama na MDD suka yi cikin haɗin gwiwa.

Mai fassara: Bilkisu