Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Tsohon ɗan ƙwallon ƙafar Chelsea, Eden Hazard ya sanar da yin ritaya daga qwallon lafa, bayan ya bar Real Madrid a ƙarshen kakar wasan da ta wuce.
Hazard mai shekara 32, ya koma Real ne daga Chelsea a shekara ta 2019 a kan fam miliyan 89, amma wasa 54 na lig kawai ya bugawa aungiyar.
Ya lashe kofin gasar firimiya biyu a Stamford Bridge.
“Dole ne ka saurari kanka, kuma ka daina buga ƙwallo a lokacin da ya dace,” inji Hazard wanda tun a watan Yuni ba shi da kulob.
“Bayan shafe shekara 16 tare da buga wasa 700, na yanke shawarar daina buga ƙwallon ƙwararru.”
Ɗan ƙwallon Belgium ɗin ya yi ritaya daga buga wa ƙasarsa ƙwallo a watan Disamban bara, bayan an fitar da ƙasar a zagayen farko na gasar kofin duniya.
A Real Madrid, Hazard ya lashe kofin zakarun Turai da kofin Super Cup da La Liga sau biyu da Copa del Rey sau ɗaya.
Sai dai ya yi abin kunya saboda ƙwallo bakwai kacal ya zura a wasa 76.
Hazard ya soma taka leda a ƙungiyar Lille inda ya ci ƙwallo 50 a cikin wasa 149 har ya lashe kofi biyu na Ligue 1 da Coupe de France a shekara ta 2011.
Ya koma Chelsea a 2012 a kan fam miliyan 32, kuma tauraruwarsa ta haska sosai a tsawon lokacinsa.
Hazard ya ci ƙwallo 110 a wasa 352 a Chelsea.
Abubuwa 11 da ya kamata ku sani game da Hazard;
- An haifi Eden Hazard a ranar 7 ga watan Janairun shekarar 1991, a La Louviere na ƙasar Belgium.
- Mahaifiyarsa, Carine, da mahaifinsa, Thierry, ‘yan wasan ƙwallon ƙafa ne. Mahaifinsa ya shafe mafi yawan aikinsa a wani kulub da ke rukuni na biyu a Louviere na ƙasar Belgium.
- Hazard ya fara wasan ƙwallon ƙafa tun yana ɗan shekara huɗu a lokacin da ya koma ƙungiyarsa ta Royal Stade Brainois. Ya shafe shekaru takwas a kulob ɗin kafin ya koma AFC Tubize. Ya koma Lille a shekarar 2005.
- Hazard ya koma Chelsea daga Lille a ranar 1 ga watan Yulin shekarar 2012, kuma ya shafe shekaru 7 a ƙungiyar. Ya koma Real Madrid ne a ranar 1 ga watan Yulin 2019. A shekarar 2015 ya zama kyaftin ɗin Belgium a kuma ya yi ritaya daga tawagar ƙasar a 2022.
- Hazard ya dokawa ƙasarsa ta Belgium wasanni 123 inda ya zura ƙwallaye 33 sannan ya taimaka aka ci 36.
- A Chelsea kuwa ya buga wasanni 352 inda ya zura ƙwallaye 110 sannan ya taimaka aka zura ƙwallaye 92.
- A Lille, Hazard ya buga wasanni 194, ya zura ƙwallaye 50 sannan ya taimaka 53.
- A Real Madrid Hazard ya buga wasanni 72 inda ya zura ƙwallaye 7 sannan ya taimaka aka ci 11.
- Hazard ya lashe kyautar Gwarzon Ɗan Wasan Ƙwallon Ƙafar Ingila a shekarar 2015.
- A Chelsea ya karɓi kyautar gwarzon 3x na shekara sau daya, a Lille kuma sau biyu.
- Hazard ya lashe gasar zakarun Turai na kakar 21/22 tare da Real Madrid, yana kuma riƙe da kofin FIFA Club World Cup na 2023 tare da Real Madrid. Hakanan kuma yana da kofunan Europa League guda 2 a kakar 2013 da 2019 tare da Chelsea.
