EFCC ta cafke jarumar Kanywood, Samha Inuwa kan zargin wulaƙanta Naira

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) yaƙi ta kama jarumar Kannywood, Samha M Inuwa bisa zargin ta da ayyukan wulaƙanta takardar naira.

A sanarwar da EFCC ta wallafa a shafinta na X, ta ce ta kama Samha ne a jiya Talata bayan samun wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta da ya nuna yadda take share majina da takardar kuɗi na N1,000.

A cewarta, hakan ya sanya ta gaggauta kama Samha bayan fitar bidiyon, inda aka cafke ta don ta je ta amsa tambayoyi.

EFCC ta ƙara da cewa, a yanzu tana tsare da jarumar yayin da ake cigaba da gudanar da bincike akan al’amarin.

Kazalika, EFCC ta ce za a tura jarumar zuwa kotu da zarar an kammala bincike domin ta fuskanci hukuncin doka.

By Babaji