
Hukumar Zaɓe a Jihar Kano ta sahale a yi wa kowane ɗan kasa rijistar zaɓe a mazaɓarsa domin sauƙaƙa wa al’umma damar mallakar katin zaɓensu.
Baturen zaɓe na Karamar Hukumar Bichi, Alhaji Abdur-Rahman Haruna Rafin-Dadi ne ya bayyana haka, yayin tattaunawarsu da Jami’ar Yada Labaran ƙaramar hukumar, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo.
Alhaji Abdur-Rahman Haruna ya ce, an koma gudanar da rijistar a dukkan mazabu a halin yanzu.
“An mayar da yin rijistar zabe daga ofishin Hukumar Zabe na Bichi zuwa kowace mazaba.” Baturen Zabe na Karamar Hukumar Bichi, Alhaji Abdur-Rahman Haruna Rafin-Dadi.
Kazalika, aikin gudanar da rijistar zaben zai tafi ne daki-daki, wato bi da bi; daya bayan daya na dukkan mazabu, inda za a ci gaba da sanar da al’umar kowace mazaba ranaku da lokaci da jami’an Hukumar Zaben za su je takanas su yi wa al’umar yankin rijistar, domin mallakar katinansu na zabe.
Bisa haka, ana kira ga daukacin al’umar Bichi, su kasa kunne ga kafafen sadarwa domin sanin lokacin da za a je kowace mazaba domin kauce wa rudu na matsalar zuwa mazabar da ba a nan lambar akwatin dangwala zabenka take ba.
A yanzu dai, tuni aka fara gudanar da wannan aiki daga ranar Litinin biyu ga watan Fabarairu na wannan shekara da ake ciki (2/2/2026). Hukumar Zaben ta Bichi ta fara ne da Mazabar Fagolo, inda za ta kammala da yankin a ranar Alhamis biyar ga wannan wata na Fabarairu 5/2/2026.
Don haka, ana bukatar iya kafatanin jama’ar yankin da suke da hakkin kada kuri’unsu a yayin zabe, da su fito kwai da kwarkwata a Mazabar tasu ta Fagolo, domin mallakar katin zabe bisa la’akari da ƙuri’arka ‘yancinka!




