EFCC ta kama jami’an hukumar tattara haraji na Jihar Katsina bisa zargin sace Naira biliyan 1.3

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Jami’an hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta’annati ta kama jami’an hukumar tattara haraji na Jihar Katsina su biyar bisa zargin karkatar da Naira biliyan 1.3 mallakar gwamnatin jihar.

Waɗanda ake zargi sun haɗa da Rabi’u Abdullahi, Sanusi Mohammed Yaro, Ibrahim Mohammed kofar soro, Ibrahim Aliyu da Nura lawal Ƙofar Soro.

An kama su bayan samun ƙorafi daga gwamnatin Katsina wanda ke zargin cewa sunyi wata hada hada tare da karkatar da kuɗaɗen da hukumar lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware wa gwamnatin jihar.

Bincike da EFCC ta gudanar ta gano Rabe tsohon daraktan hukumar kuma yanzu sakatare ne na dindindin a hukumar,ya amince a buɗe asusun banki da suna “BORIS” a bankin Sterling.

Haka kuma Rabe ya naɗa Sanusi Mohammed Yaro a matsayin daraktan asusun inda akai ta karkatar da kuɗaɗen ta wani kamfani mai suna “NADIKKO GENERAL SUPPLIERS”mallakar Nura Lawal Kofar Soro mataimakin daraktan a hukumar tattara haraji na jihar.

EFCC ta ƙara gano cewa kamfanin Nura Kofar Soro ta zana hanyoyin karkatar da kuɗaɗen da ake zargin an sace .

Yanzu waɗanda ake zargi da wannan sata na hannun hukumar EFCC a ofishin su da ke Kano.

Nan gaba kaɗan za a gurfanar da su gaban kotu.