Zuwan Gwamna Abba gwamnatin Kano ne ta fara amfana da harkokin NDE – AVM Ibrahim

Daga RABIU SANUSI a Kano

An bayyana cewa zuwan gwamnatin Abba Kabir Yusuf ne bayan tafiyar Gwamnatin Dakta Rabiu Musa Kwankwaso Jihar Kano ta ke samun damar samar ma al’umma hanyoyin dogaro da kai.

AVM Ibrahim Umaru ya bayyana haka ne a wajen ƙaddamar da shirye-shiryen da ake yi na ɗaukar matasa kimanin 6000 da za’a koyar da sana’o’i daban-daban da dogaro da kai a shiyyar Kano ta tsakkiya da ta Kudu.

AVM Ibrahim Umaru Rtd wanda ya samu wakilcin mataimakin darakta na musamman na ma’aikatar kula da ayyuka na musamman a fadar gwamnatin Kano, Alhaji Habibu Madigawa.

Babban daraktan ya ce kamar yadda mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf da tawagar shi suke gabatar da yaƙin neman zaɓe, sun yi alƙawura daban daban wajen nemo ma al’ummar Jihar Kano madogara,wannan na cikin wannan alƙawura da a ka ɗauka.

”Yau zamu ƙara tabbatar maku cewa babu abinda ke a zuciyar mai girma gwamna wanda ya wuce ya cika maku alƙawarin da ya ɗaukar maku.

”Wannan hanya itace za ta taimaka ma matasan mu idan sun tsaya sunyi abin da ya kamata wajen koyon abinda za su dogara da kansu musamman yadda rayuwa tayi tsada.

Daraktan ayyuka na musamman ya kuma buƙaci waɗanda suka samu wannan damar da suyi amfani da wannan damar dan taimakon Kan su da taimakon iyalan su.

”Kun dai san yanayin yadda ƙasar ta zama a halin yanzu komi yayi wahala amma kasancewar mai girma Gwamna yana kishin al’ummar shi yasa yake ƙoƙari wajen kawo sauyi a rayuwar mutanen Kano, inji AVM Ibrahim Umaru Rtd.

Shima da yake na shi jawabin shugaban hukumar kula da bada horo da samar da hanyar dogaro da kai ta NDE Jihar Kano Yarima Sa’adu Iya, ya bayyana cewa lallai wannan aiki da suke yi a matakin Ƙasa zuwa Jihar Kano zai taimaka matuƙa wajen bai wa matasa maza da mata hanyar dogaro da kan su.

Yarima Iya yace a wannan gaɓar za su koyar da Mlmutanen Kano kimanin 4800 sana’o’i daban-daban dan dogaro da kansu.

Haka kuma shugaban na NDE ya ƙara da cewa wannan yunƙuri na gwamnatin Abba Kabir Yusuf na ɗaya daga cikin jajircewar gwamnan na ganin al’umma su samu abin yi dan haka dole a yaba mai.

Yarima Iya ya ɗora da batun cewa yadda gwamna ya samu wakili jajirtace AVM Ibrahim Umaru Rtd yasa ake gane motsin tafiyar gwamnatin shi ta wannan hanyar da ake buƙatar aiwatar wa.

”Muna matuƙar godiya bisa wannan jajircewa ta gwamnatin Kano ƙarƙashin wakilcin babban daraktan Kula da ayyuka na musamman, muna fatan sauran wakilan Gwamna za su yi koyi da shi dan rage ma mai girma gwamna aiki.

Shima jagoran kula da wannan yunƙuri da yake magantuwa Hon Abdullahi Amne ya bayyana cewa lokacin jagoran Kwankwasiyya yana ɗaya daga cikin waɗanda suka amfana da wannan tsari.

Amne wanda ya cigaba da cewa a lokacin da aka ɗauke su wannan bita da yawan abokan shi sunyi suka akan shi da cewa babu abinda za su samu a wannan tsari yanzu gashi yana ɗaya daga cikin jagorori.

A nashi jawabin shugaban Ƙaramar hukumar Gwarzo Hon Mani Tsoho da ya samu wakilcin ɗaya daga cikin kansilolin da ke jagoranta wannan sashe na nema ma matasa hanyar dogaro da kai Hon Nazifi Salihawa yace, lallai wannan yunƙuri na gwamnatin Abba Kabir Abin a yaba ne.

Hon.Nazifi Salihawa ya kuma buƙaci waɗanda suka samu wannan dama dasu tsaya su koyi abinda ya kamata.

Wakilin Shugaban ƙaramar hukumar ya kuma ƙara gode wa mai girma gwamna da daraktan kula da ayyuka na musamman dama hukumar NDE wajen ƙoƙarin sauya rayuwar al’ummar Jihar Kano.

Wasu daga cikin ƙananan hukumomin da aka fara zaƙulo mutanen da zasu rabauta da wannan horo sun haɗa da Tarauni,Kumbotso,Ungoggo,Nasarawa,Dala,Gwale,Fagge da ƙaramar hukumar Birni.

Haka zalika ƙananan hukumomin Kabo,Bagwai,Tsanyawa,Shanono da dai sauran wasu ƙananan hukumomin da aka haɗu a ƙaramar hukumar Gwarzo wajen miƙa ma waɗanda za su amfana da tsarin da su cike fom tare da basu bayanai akan yadda horon zai gudana da Ƙa’idojin da suke kan tsarin horarwar.