El-Ghazi ya maka Mainz a kotu kan sallamarsa daga ƙungiyar

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ɗan wasan ƙasar Holland Anwar El Ghazi na shirin ɗaukar matakin shari’a a kan tsohon ƙungiyarsa Mainz saboda korar da aka yi masa ba bisa ƙa’ida ba.

Mainz ta soke kwantiragin El Ghazi a ranar 2 ga Nuwamba bayan wasu jerin rubuce-rubucen da ya yi a shafukan sada zumunta game da rikicin Isra’ila da Gaza.

Mainz ta ce tawagar lauyoyin El Ghazi ne suka sanar da ita game da lamarin.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta ƙara da cewa ba za ta ƙara yin tsokaci ba domin shari’a ce da ke gudana a halin yanzu.