Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa halin ƙuncin da ƙasar nan ke fama da shi a halin yanzu ya samo asali ne daga gwamnatin Muhammadu Buhari, wanda wanda ya bar wa Tinubu gadon ƙasar cikin mawuyacin halin tattalin arziki.
Yayin da yake jawabi a taron shekara-shekara na hukumar leƙen asiri ta rundunar tsaro ta 2023 a Abuja a ranar Litinin, Ribadu ya amince da matsananciyar matsalar kuɗi da ta shafi kasafin kuɗi amma ya tabbatar wa al’ummar ƙasar cewa Gwamnatin Tarayya ta ƙuduri aniyar ci gaba da samar da ingantaccen tsarin tsaro.
“Ina tabbatar muku cewa gwamnatin tarayya ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin an samar da ingantaccen tsarin kula da tsaro don magance qalubalen da ake fuskanta a wannan lokaci.
“Yana da muhimmanci a gareku ku sani cewa mun gaji gwamnati a cikin wani irin yanayi mai matuƙar wahala, a zahiri ƙasa nan tana cikin fatara, babu kuɗi, har ta kai ga cewa duk kuɗin da muke samu a yanzu; muna mayar da abin da aka ɗauka na bashi.
“Amma wannan gwamnatin tana yin iya ƙoƙarinta don ganin ta cika buƙatunmu, musamman sojoji, kuma na yi imanin cewa ku shugabannin za ku iya bada shaida kan hakan,” Ribadu ya ce.
Ya kuma yaba wa rundunar sojin ƙasar bisa jajircewar da suka yi wajen tunkarar ƙalubalen tsaro da ake fama da shi a ciki da wajen Nijeriya, inda ya yi nuni da cewa an samu sauyi mai kyau da kuma ci gaba.
Da yake kira da haɗin kai da goyon bayan hukumomin tsaron ƙasar, Ribadu ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa idan aka yi azamar shugabanci, al’ummar ƙasar za su shawo kan matsalolin da suke ciki.
“Mu haɗu a dunƙule, mu ci gaba da tallafa wa dakarunmu da sauran jami’an tsaro da wannan aiki na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasarmu.”
Shugaban hukumar leƙen asiri ta ƙasa, Manjo Janar Emmanuel Undiandeye, a martanin da ya mayar, ya tabbatar da aniyar hukumar na yin amfani da ƙarfin tsarin hafsoshin tsaro domin cimma manufofin tsaron ƙasa.
Taron ya samu halartar manyan baƙi da suka haɗa da ministan tsaro, ƙaramin minista, da wasu manyan jami’ai a ma’aikatar tsaro.
