‘Yan sanda sun yi musayar wuta da ɓarayin daji a Zamfara

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A qarshen makon da ya gabata ne jami’an ‘yan sanda suka yi artabu da ‘yan bindiga a ƙauyen Gada da ke Ƙaramar Hukumar Bunguɗu a jihar Zamfara, inda aka kashe da dama daga cikin ‘yan bindigar, wasu da dama kuma suka gudu da harbin bindiga.

‘Yan bindigar ɗauke da muggan makamai sun hau babura da dama, inda suka mamaye al’ummar Gada, inda suka kashe mutanen yankin 8 tare da yin awon gaba da shanu da dama.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar, ya ce sun samu nasarar fatattakar ‘yan bindigar, kuma sun kashe da dama yayin da wasu da dama suka gudu da harbin bindiga.

Ya ce sun ƙwato shanu 10 daga hannun masu satar shanu da wasu tumaki inda suka ce ‘yan bindigar sun kashe mutanen yankin 6 ne kawai.

A cewarsa a lokacin da muka samu labarin, DPO na yankin ya tara mutanensa da ‘yan banga da suka tunkari ‘yan bindigar.

Abin takaici, ‘yan banga 6 ne suka mutu a yayin arangamar sannan 7 sun samu raunuka. Amma Alhamdulillahi mun kashe da yawa daga cikin ‘yan bindigar, wasu da dama kuma sun gudu da raunuka sakamakon harbin bindiga.”

Sai dai wani wanda ya tsira da ransa ya shaida wa manema labarai cewa, ‘yan bindigar ɗauke da muggan makamai sun kai wa al’ummar garin hari ne da misalin qarfe 1 na safe zuwa 3 na dare inda suka kashe mutane 8.

Ya ce waxanda suka jikkata a harin, an garzaya da su asibiti domin yi musu magani a Gusau.

‘Yan bindigar ba su yi garkuwa da kowa ba, amma sun tafi da shanu da yawa. Wasu shanun sun dawo daga baya. Ba mu da isassun jami’an tsaro,” inji shi.

Wani ɗan majalisar tarayya mai wakiltar yankin Hon Abdulmalik Zubairu ya ce a ko da yaushe ‘yan bindigar da ke kashe jama’a da kuma cutar da jama’ar mazavarsa ne.

Ya ce jami’an tsaro a yankin ba su isa ba, inda ‘yan sanda 4 ne kawai.

‘Yan bindiga sun kai hari a Zamfara, musamman a mazaɓar Bungudu-Maru, shine babban abin da ya damemu, yana ba mu damuwa sosai,” inji shi.

By Editor