
Daga BELLO A. BABAJI
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i, ya zargi magajinsa na kujerar, Uba Sani, da sauya akalar kuɗaɗen ƙananan hukumomin jihar wajen sayen gidaje a ƙasashen Seychelles da Afirka ta Kudu da Birtaniya.
El-Rufa’i ya yi zargin ne a yayin hira da gidan rediyon Freedom a Kaduna, inda ya ce gwamnan ya canza kuɗaɗen ne zuwa daloli a yayin sayen gidajen.
Ya ce, shi a zamaninsa bai taɓa tsoma baki a kuɗaɗen ƙananan hukumomi ba, kuma ko da kwabo ɗaya bai taɓa ɗauka ba, ya na mai cewa ciyamomin zamanin nasa suna raye, za su iya bada shaida.
Tsohon gwamnan ya ƙara da cewa, sun ɗauka bai san abinda ya ke faruwa ba a yayin da aka sauya akalar kuɗaɗen, inda bayyana cewa ya san komai game da lamarin.
Ya kuma ce, bai taɓa karɓar cin hanci a wajen kowane ɗan kwangila ba, ya na mai ƙalubalantar a tona masa asiri idan akwai inda aka san ya karɓa.
Kazalika, ya zargi Gwamna Uba Sani da karɓar kaso 40 daga kowane ɗan kwangila kafin ya amince da ba shi aiki a jihar.
Saidai, APC ta na ganin El-Rufa’i yana bayyana ire-iren zarge-zargen nan ne akan ƴaƴan jam’iyyar duba da cewa bai samu muƙamin minista ba a Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, kamar yadda Sakataren yaɗa labaranta, Felix Morka ya bayyana a shafinsa na X.