Faɗi alkhari ko ka yi shiru

Spread the love

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.

’Yan uwa masu daraja, wannan wasiƙa tunatarwa ce ga zuciyarmu da harshenmu a wannan zamani da kalma guda ke iya gina rayuwa ko rusa ta. Addinin Musulunci ya ɗora wa kalma matsayi mai girma, domin daga baki ne alkhairi ke fita, kuma daga nan ne sharri ke bazuwa. Saboda haka Manzon Allah (SAW) ya yi gargaɗi mai tsanani da cewa: “Duk wanda ya yi imani da Allah da Ranar Lahira, to ya faɗi alkhairi ko kuma ya yi shiru.” Wannan hadisi shi ne tubalin wannan wasiƙa.

A kwanakin nan, al’ummar mu sun shiga jimami da firgici sakamakon mummunan kisan uwa da ’ya’yanta shida a unguwar Dorayi da ke Kano. Wani lamari ne da ya girgiza zukata, ya tada hawaye, ya kuma bar tambayoyi masu yawa a cikin al’umma. Irin wannan bala’i ba ƙaramin jarrabawa ba ne, kuma ya kamata ya sa mu ƙara natsuwa da tausayi, ba wai ƙara zuba gishiri a rauni da kalaman zuƙi-ta-mallo ba.

Sai dai abin takaici, a daidai lokacin da jama’a ke jimami da addu’ar Allah Ya tona asirin waɗanda suka yi wannan ɗanyen aiki, sai aka samu wasu da suka mayar da lamarin dandali na neman suna da jan hankali. Wani mutum ya bayyana a wani faifan bidiyo yana faɗin cewa shi ne ya ga masu laifin, shi ne ya kira jami’an tsaro daban-daban — ’yan sanda, DSS, Kwastom, Immigration har da ’yan sa-kai — alhali daga baya aka gano cewa ba gaskiya ba ne. Maganganunsa sun rikita jama’a, sun ɓata alƙiblar tattaunawa, kuma daga ƙarshe suka jawo masa ba’a da tsokana a kafafen sada zumunta, inda wasu suka laƙaba masa suna “Sarkin ƙaryar ƙasar Hausa.” Ba ina goyon bayan tsokanar da mutane da suka riƙa yi masa ba ne, amma misali ne mai ƙarfi da ke nuna cewa, ya kamata mutane su riƙa iya bakin su.

Wannan lamari ya zama darasi mai girma ga kowa da kowa. Allah Maɗaukakin Sarki ya ce a cikin Al-ƙur’ani: “Ya ku waɗanda ku ka yi imani, ku ji tsoron Allah kuma ku faɗi magana mai daidai.” (Suratul Ahzab 33:70). Haka kuma a wani wuri ya yi gargaɗi: “Ya ku waɗanda ku ka yi imani, idan mai fasiƙanci ya zo muku da labari, ku tantance, kada ku cuce mutane saboda jahilci, sannan ku zama masu nadama.” (Suratul Hujurat 49:6).

Waɗannan ayoyi guda biyu sun isa su zama dokar rayuwa a gare mu, musamman a wannan zamani na kafafen sada zumunta inda labari ke tafiya cikin sakan kaɗan. Mutum zai rubuta abu ba tare da bincike ba, a yaɗa shi, a gaskata shi, daga ƙarshe a gano ƙarya ce — amma cutar da aka yi wa suna, iyali ko al’umma ba ta komawa baya.

Yin ƙarya ba ƙaramin laifi ba ne a Musulunci. Manzon Allah (SAWW) ya ce ƙarya tana kai mutum zuwa fajirci, fajirci kuma yana kai mutum zuwa wuta. Amma abin da ya fi muni shi ne ƙaryar da ake yi a lokacin bala’i. Lokacin da iyalai ke kuka, yara suka rasa uwa, al’umma ke cikin tashin hankali, sai wani ya mayar da wannan yanayi tamkar wasan kwaikwayo ko dandalin neman shahara. Wannan ba rashin hankali kaɗai ba ne, rashin tausayi ne.

Yawan son a ji sunan mutum a kafafen sada zumunta ya jefa mutane da dama cikin halin faɗin abin da ba su sani ba. A Musulunci, ba a auna mutum da yawan mabiyansa ba, ana auna shi ne da gaskiyarsa da tsoron Allah. Mutumin da ya iya cewa “Ban sani ba” ya fi wanda ke cika duniya da surutu marar tushe.

Bayan haka, irin waɗannan ƙaryace-ƙaryace na iya kawo cikas ga binciken jami’an tsaro. Lokacin da ake yaɗa bayanai marasa tushe, ana iya ɓata alƙiblar bincike, a kuma jefa jama’a cikin ruɗani da tsoro. Addinin Musulunci ya koyar da mu kula da maslahar al’umma gaba ɗaya, ba son zuciyar mutum ɗaya ba.

Abin takaici ne yadda a ƙarshe lamarin ya juya ya koma abin dariya da ba’a a shafukan sada zumunta, kamar ma an manta da ainihin abin da ya faru. Duk da cewa mutumin ya yi kuskure babba, ya kamata mu ma mu kula da harshenmu. Zagi, tsangwama da wulaƙanci ba su gyara kuskure; sau da yawa suna ƙara lalata tarbiyya ne kawai. Manufar darasi ita ce gyara al’umma, ba ƙara yawan laifi ba.

Maimakon mu yi ta yaɗa bidiyo da saƙonnin ba’a, ya kamata mu riƙa yaɗa darasin da ke ciki: Kada mu faɗi abin da ba mu tabbatar ba. Kada mu nemi suna ta hanyar hawa kan bala’in wasu. Kada mu ɗauki jimamin al’umma tamkar wata dama ta yin suna.

Iyaye su ƙara kula da tarbiyyar ’ya’yansu a kan amfani da kafafen sada zumunta. Malamai su ƙara wa’azi a kan illar jita-jita da ƙarya. ’Yan jarida da masu wallafa labarai su tsaya tsayin daka wajen tabbatar da sahihancin abin da suke fitarwa. Gwamnati ma tana da rawar takawa ta hanyar wayar da kai da kuma hukunta masu yaɗa labaran ƙarya da gangan, musamman idan sun shafi tsaro ko rayukan jama’a.

Kafin ka danna “send” ko “post”, ka tambayi kanka: Shin wannan gaskiya ne? Shin yana da amfani? Shin zai taimaka ko zai cutar? Idan babu tabbas, shiru ibada ne. Shiru kariya ne. Shiru hikima ne.

Mu tuna cewa kalmominmu ana rubuta su. Mala’iku suna rubuta komai, kamar yadda Allah ya faɗa: “Babu wata magana da mutum zai furta face akwai mai sa ido a shirye.” (Suratul ƙaf 50:18). Wannan ya isa ya sa mu ji tsoron Allah a kan abin da muke faɗa, ko da kuwa a rubuce ne a waya.

Allah Ya jikƙan waccan uwa da ’ya’yanta shida da aka rasa a Dorayi, Ya ba iyalansu haƙuri, Ya kuma tsare mu daga faɗin abin da zai cutar da mu a duniya da lahira. Ya sa mu zama masu amfani da harshenmu wajen yaɗa alkhairi, gaskiya da tausayi.

Idan ba za mu faɗi alkhairi ba, to mu yi shiru.

Wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD, ƙaramin Edita, Blueprint Manhaja. 07066778190.

By ukarofi