
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kotun Ƙwadago ta Ƙasa ta haramta wa Ƙungiyar Ƙwadago (NLC) da Ƙungiyar Kasuwanci (TUC) da wasu ɓangarori uku shiga kowane irin yajin aiki ko zanga-zanga a Babban Birnin Tarayya Abuja.
Mai Shari’a Emmanuel Subilim, ya bada umarnin wucin-gadi ne a ranar Litinin bayan sauraron buƙatar gaggawa da Ministan FCT, Nyesom Wike, da Hukumar Gudanarwar FCT suka shigar.
Umarnin ya shafi jami’an ƙungiyoyin ƙwadago da suka haɗa da kakakin NLC, Benson Upah, Sakataren TUC, Nuhu Toro, da Shugaban NLC na FCT, Stephen Knabayi.
Sannan, rahotanni sun ce kotun ta haramta wa waɗanda ake ƙara da wakilansu ɗaukar duk wani matakin yajin aiki ko zanga-zanga har sai an saurari buƙatar kotu ta gaba.
Kazalika, kotun ta umurci hukumomin tsaro da su tabbatar da cewa babu wata tangarda ga doka da oda a Abuja.
A cewar masu ƙara, an shigar da ƙarar ne saboda fargabar cewa shirye-shiryen zanga-zanga da aka tsara za su iya haddasa rikici, cikas ga zirga-zirga da kuma take haƙƙin mazauna Abuja.
