Gwamnatocin Tarayya da na jihohi da ķananan hukumomi sun raba tiriliyan N1.681 a Afrilu

Spread the love

Daga BELLO A.BABAJI

Jimillar Naira tiriliyan 1.681 daga kudaden Harajin Asusun Tarayya na watan Afrilu ne aka raba a tsakanin Gwamnatin Tarayya, na jihohi da na ķananan hukumomi.

An gudanar da rabon ne a taron watan Mayu na Kwamitin Asusun Tarayya (FAAC) a Abuja, ranar Juma’a.

A sanarwar da Kakakin Kwamitin, Bawa Mokwa ya fitar, ya ce kuďin ya ķunshi wanda aka tattara daga harajin aiki (na ķa’ida) – biliyan N962.882 da na harajin VAT – biliyan N598.077 sai na harajin hadada, EMTL – biliyan N38,862 da kuma na banbance-banbancen kasuwanni (Exchange Difference) – biliyan N81.407.

A wata takarda da FAAC ya fitar, Gwamnatin Tarayya ta samu Naira biliyan 565.307 yayin da gwamnatocin jihohi kuma suka samu biliyan N556.741.

Sai kananan hukumomi, waɗanda suka samu jimillar biliyan N406.627, yayin da biliyan N152.553 kuma aka raba wa jihohi masu amfana daga harajin albarkatun ƙasa.

Daga cikin Naira biliyan 962.882 na harajin aiki kuwa, Gwamnatin Tarayya ta samu biliyan N4131.307 yayin da gwamnatocin jihohi suka samu N218.765bn.

Kananan hukumomi kuma sun samu Naira biliyan 168.659 da kuma biliyan N144.151 ga jihohin da ke amfana daga harajin albarkatun ƙasa.

A biliyan 598.077 na harajin banki na VAT kuwa, Gwamnatin Tarayya ta samu biliyan N89.712, sai na jihohi waɗanda suka samu N299.039bn, yayin da na kananan hukumomi suka samu biliyan N209.327.

Jimillar N5.829bn ta tarayya ta karɓa daga N38.862 na harajin hadadar banki na EMTL, inda na jihohi suka samu biliyan N19.431, sai biliyan N13.602 ga kananan hukumomi.

Haka kuma a biliyan N81.407 na harajin ‘Exchange Difference’, ta tarayya ta samu N38.459bn, sannan na jihohi kuma N19,507bn. Na kananan hukumomi shi ne biliyan N15.039bn, sannan kuma biliyan 8.402 ga jihohi masu amfana daga harajin albarkatun ƙasa.

By Babaji