FAAC: Gwamnatin Tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi sun raba Tiriliyan N1.703 a Junairu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Asusun Kasafta Kuɗaɗen Tarayya, FAAC ya ce ya raba kuɗaɗen shiga da adadinsa ya kai Naira Tiriliyan 1.703 a tsakanin Gwamnatocin Tarayya da na jihohi da ƙananan hukumomi a watan Junairu.

Daraktan Labarai na ofishin Antoni-Janar na Ƙasa, Bawa Mokwa ya bayyana haka a wata takarda biyo bayan kammala zaman FAAC a ranar Alhamis.

Ya ce, kuɗaɗen sun haɗa da harajin zamantakewa (Biliyan N749.727) da na VAT da adadinsa ya kai Naira biliyan 718.781.

Haka kuma akwai na banki, wato EMTL, wanda ya tara biliyan N20.548 da kuma na faɗaɗawa da ya kai biliyan N240.

Jimillar kuɗin da aka tara a Junairun ya kai Naira Tiriliyan 2.641.

Sanarwar ta ce, Gwamnatin Tarayya ta samu biliyan N552.591 yayin da gwamnatocin jihohi suka samu biliyan N590.615. Su kuma na ƙananan hukumomi suka samu Naira biliyan 434.567.

By Babaji