Ramadan: Sarkin Musulmi ya ce a fara duba wata daga ranar Juma’a

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Ƙoli kan Harkokin Musulunci ta Ƙasa (NSCIA), Mai Alfarma Sa’ad Abubakar, ya yi kira ga al’umma da su fara neman watan Ramadan daga ranar Juma’a don fara azumin watan na shekarar hijiriyya ta 1446.

Sanarwar ta fito ne daga ofishin Shugaban Kwamitin Shawarwari na Harkokin Addini na Majalisar Sarki a Sakkwato, Farfesa Sambo Junaidu.

Ya ce, Sarki Sa’ad Abubakar ya yi addu’ar fatan kariyar Allah da samun albarkarSa ga al’ummar musulmi a yayin da suke shirin shiga wata mai alfarma.

Sanarwar ta kuma fitar da lambobi da za a aiko da rahoton ganin watan kamar haka; 08037157100, 08066303077, 08035965322, 08099945903, da kuma 07067146900.

By Babaji