Zargin aikata alfasha da Akpoti ta yi wa Akpabio ihu ne bayan hari – Kwamared Salihu Ɗantata

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Tsohon Mashawarcin ɗan Majalisar Wakilai a Abuja kan yaɗa Labarai da Leƙen asiri, Kwamared Salihu Ɗantata ya bayyana zargin aikata alfasha da Sanata Natasha ta yi akan Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio a matsayin yin magani bayan mutuwa.

Ya ce, sai da ta samu matsala da Shugaban Majalisar kafin ta fitar da zargin, wanda hakan ya kai ta ga saɓa wa zaman majalisar da dokokinta.

Kwamared Salihu a wata takarda, ya ƙalubalanci sanatar, a inda ya ce mai yasa ba ta fitar da batun ba sai yanzu da ba lallai ƴan Nijeriya su yarda da abinda ta faɗa ba.

Ya kuma ce, majalisa ta fi ƙarfin a yi zarge-zargen kan titi a cikinta ba tare da gabatar da hujja karɓaɓɓiya ba.

Kwamared Salihu Ɗantata ya ƙara da cewa lallai sai ta bada shaida karɓaɓɓiya kamar bidiyo ko makamancinsa da zai tabbatar da zargin nata.

Har’ilayau, ya ce irin zargin shi ne wanda tsohuwar Darakta-Manaja ta Hukumar Kula da Yankin Neja-Delta ta yi a lokacin da Majalisar ta gurfanar da ita don yin bincike akan ta sadda Akpabio ya ke Ministan Harkokin Neja-Delta.

Ya kuma yi kira ga ƴan Nijeriya da su yi hattara game da saurin ɗaukar bayanan da ba a kai ga tabbatar da su ba.

By Babaji