Waiwaye: Tsohuwar Shugabar NDDC ta hakaito yadda ta mari Akpabio kan neman ta da alfasha

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A makon nan ne Sanatar PDP daga Jihar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan ta zargi Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da yunƙurin neman ta da alfasha.

Natasha ta yi zargin cewa, sau da yawa Akpabio ya kan kira ta da tsakiyar dare yana mata maganganun soyayya, wanda ta kan tashi mijinta tare da sanya ansakuwwa don jiyar da shi abinda ya ke faɗa mata.

Ta bayyana ƙin amincewa da buƙatarsa da ta yi a matsayin dalilin da yasa aka tsane ta a majalisar.

Natasha ta bayyana hakan ne a yayin wata hira da gidan talabijin na Arise a ranar Juma’a, inda ta yi bayanin abinda ya faru dalla-dalla a ranar 8 ga watan Disambar 2023 a lokacin da suka kai wa Akpabio ziyara ita da mijinta a gidansa.

Ta ce, duk da cewa mijinta yana tare da su, amma ya yi ta ƙoƙarin yi mata abubuwa na rashin ɗa’a.

Haka kuma ta ce, ya taɓa faɗa mata cewa zai riƙa kula da ita idan ta amince saboda a riƙa karɓar batutuwanta a zauren majalisar.

Tuni dai Natasha ta shigar da ƙara akan Akpabio da babban mataimakansa, Mfon Patrick kan zargin su da ɓata mata suna, inda ta nemi a biya ta biliyan N100 da kuma miliyan N300 da ta kashe a harkokin shari’a.

A wani ɓangaren, tsohuwar Darakta-Manajar riƙon ƙwarya ta Hukumar Ci-gaban Yankin Neja-Delta (NDDC), Joy Nunieh, ta yi ikirarin cewa ta tsinke Akpabio da mari a ranar 20 ga watan Yulin 2020, a lokacin da ya ke Ministan hukumar, bayan ya neme ta da aikata alfasha.

Ta tabbatar da aukuwar lamarin ita ma a gidan telebijin na Arise a yayin da ake tsaka da batun Natasha, inda ta ce ta mare shi ne a gidan saukar baƙi dake Apo a Abuja.

Saidai, a yayin da ya ke ƙoƙarin kare batun, Akpabio ya ce lallai Nunieh ta na da buƙatar ganin likita akan kalaman da ta yi akansa waɗanda ya ce an ƙirƙire su ne don a ɓata masa suna.

By Babaji