Fadar Shugaban ƙasa ta buƙaci Bala ya janye barazanar da ya yi wa Tinubu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Fadar Shugaban ƙasa ta buƙaci gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya janye barazanar da ya yi wa shugaban ƙasa Bola Tinubu kan batun sake fasalin haraji.

Wata sanarwa a ranar Litinin mai taken; martani a kan ‘Za mu nuna wa Tinubu Launinmu na Gaskiya’ da mai ba da shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da sadarwar jama’a, Sunday Dare ya raba a kan hannun ɗ, ya bayyana barazanar Mohammed a matsayin “mai tayar da hankali.”

Hakan ya biyo bayan sanarwar da gwamnan ya fitar ya ce shugaba Tinubu yana kira ne da a kawo rashin zaman lafiya idan ya ci gaba da sauye-sauyen haraji.

Gwamna Mohammed ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga al’ummar Kirista a Bauchi.

Ya yi gargaɗin cewa idan aka ci gaba da waɗannan tsare-tsare, yankin arewa zai “nuna ainihin launukansa” don mayar da martani.

Mohammed ya kuma jaddada cewa irin waɗannan sauye-sauyen na iya haifar da koma baya a fannin tattalin arziki, inda ya ƙara da cewa sauye-sauyen ya fifita jiha ɗaya kacal na tarayyar.

Ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta sake nazari tare da aiwatar da wasu tsare-tsare masu amfani.

Duk da haka, fadar shugaban ƙasa ta ce, “Muna roƙonsa da ya janye waɗannan kalamai na cin karo da juna tare da mayar da hankalinsa ga tattaunawa mai inganci da Gwamnatin Tarayya game da duk wata damuwa game da dokar sake fasalin haraji.

“Wannan magana mara daɗi ba ta wakiltar muryar gamayya ta Arewacin Nijeriya. Arewa, kamar sauran yankuna, tana neman tsarin mulki na haɗin gwiwa da kuma kyakkyawar alaƙa da Gwamnatin Tarayya don magance ƙalubalen ƙasarmu.”

By ukarofi