Muna da masaniya kan jajircewar Hon. Doguwa wajen aiki – Injiniya Abdulrazak

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano

Babban sakataren ma’aikatar albarkatun ruwa ta Jihar Kano, Injiniya Abdulrazak Haruna, ya bayyana cewa suna da cikakkiyar masaniya da labarin cewa sabon kwamishinan albarkatun ruwa na Jihar Kano Hon. Haruna Umar Doguwa, jajirtacce ne wajen aiki da bauta wa al’umma, da kuma biyayya da dokokin aiki na gwamnatin Kano ƙarƙashin shugabancin Alhaji Kabir Yusuf.

Ya ce wannan dalili ya sa suke farin ciki da zuwan shi wannan ma’aikata, kuma ɗaukacin ma’aikatan wannan ma’aikata za su bashi goyan baya ɗari bisa ɗari, domin ciyar da ma’aikatar da Kano baki ɗaya, kamar dai yadda babban Sakataran Injiniya Abdulrazak Haruna ya bayyana a lokacin da ‘yan uwa, masoya, ma’aikata, suka raka shi sabuwar ma’aikatar da gwamnan Kano ya tura shi a tsakiyar makon nan.

Injiniya Haruna ya ce kamar yadda suka yi aiki da tsohon kwamishina Hon. Ali Haruna Makoɗa, wanda shi ne sabon kwamishinan Ilimi na Kano a yanzu, ya ce a lokacin da ya ke ma’aikatar ruwa, sun zauna da shi lafiya, kuma mutum ne wanda ya ke kishin aiki da jajircewa, duk da yake bai daɗe da shi ba, amma ya ce ya fahimci mutum ne mai ƙwazo a aikinsa a duk inda ya samu kansa, kuma suna musu fatan alkairi da fatan cigaban Kano da na Nijeriya baki ɗaya.

A ƙarshe shi ma sabon kwamishinan ruwa Hon. Umar Haruna Doguwa, ya yaba wa gwamnatin Kano kan damar da ta bashi na zama kwamishina har sau uku a shekarunsa na rayuwa kuma zai yi iya ƙoƙarinsa wajen ɗorawa akan inda tsohon kwamishina Gwani Ali Haruna Makoɗa ya tsaya wajen samar da wadataccan ruwan sha a Kano bisa buri da ƙudiri na warware matsalar ruwa da sauran matsaloli na mutanen Kano a wannan lokaci.

Hon. Doguwa ya samu rakiyar Shugaban ƙaramar Hukumar Doguwa Hon. Abdulrashid Ridwan Doguwa, da Kakakin kansilolin ƙaramar hukumar Hon. Salim Shu’aibu Maraku, da Naziru Abdullahi Doguwa, sai shugaban jam’iyya NNPP Auwalu Hussaini Doguwa, da sauransu.

By ukarofi