Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Babbar jam’iyyar hamayya a Nijeriya, PDP ta ce nan ba da jimawa ba za su tuntuɓi tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa kwankwaso, domin ya sake komawa jam’iyyar a yi tafiya tare domin ganin bayan jam’iyyar APC mai mulki a ƙasar.
Muƙaddashin shugaban jam’iyyar, Ambasada Umar Iliya Damagun ne ya bayyana haka a hirarsa da BBC, yayin da yake mayar da martani kan kalaman da Kwankwason ya yi na cewa jam’iyyar, PDP ta mutu, kuma ba za ta iya wata nasara ba a nan gaba.
Ya jaddada cewa a yanzu haka a shirye suke su karbi duk wasu ‘ya’yansu da suka yi fushi suka tafi wasu jam’iyyu, ciki har da Sanata Kwankwanson.
”Mutum zai iya faɗin ra’ayinsa, amma ina so in tuna masa baya, a lokacin da suka bar jam’iyyar PDP a 2015, in ba ta mutu ba a wancan lokacin, a 2015, a lokacin da suke ganin sun yi mata illa to ba n ga dalilin da za a ce ta mutu ba yanzu,” inji shugaban.
Ya ƙara da cewa, ”kuma kar ka manta jam’iyyar PDP ita kaɗai ce ke iya cin zaɓe idan aka cire masu mulki.”
Damagun ya ce shi kansa Kwankwason da ya ce PDP ta mutu, ai bai yi wa kansa adalci ba, domin ai ya ɗauki jam’iyya amma jiha nawa ya ci ?
Shugaban na riƙo ya kuma bugi ƙirji da cewa jam’iyyarsu ta PDP ita ce har yanzu bayan shekara 26 take amsa sunanta na PDP ba ta sauya ba, kuma take da gwamnoni dasanatoci zababbu a kowane sashe dabangare na Nijeriya.
Ya ce yau a Nijeriya idan aka cire PDP, aka hada jam’iyyu hudu ba za su iya cin zabe ba.
Dangane da magar na Kwankwason ya yi cewa an ci musu fuska a jam’iyyar ta PDP a baya saboda haka ya kawar da duk wata magana ta hada kai da su domin zaben 2027, Ambasada Damagun ya ce lalle haka ne wasu maganganun na Kwankwaso ya yi gaskiya ne domin shi kansa a lokacin da tsohon gwamnan na Kano yake yunkurin barin jam’iyyar lokacin shi yana matsayin mataimakin shugabanta na kasa shiyyar arewa ya yi iya kokarinsa na sasantawa amma abin ya ci tura.
”Amma dai duk da haka ba shi da jam’iyyar da ta fi PDP domin idan ka duba ita ta rene shi, ita ta kawo masa siyarsa ta kai inda yau ta kai, har gobe ba ma cire tsammani zai iya zuwa a yi tafiya da shi mu karkade jam’iyyarmu mu fuskanci wannan azzalumar gwamnati,” in ji shugaban.
Shugaban na PDP, ya ce idan Allah Ya yarda nan ba da jimawa ba za su tuntubi, Kwankwason duk cewa ya san a fusace yake, kuma ya san abin da yake so zai yi wuya ya samu a waccan jam’iyyar da yake.
Ya ce jam’iyyarsu ta PDP jam’iyya ce da kodayaushe take karbar duk wani danta da aduk lokacin da ya yi fushi ya tafi idan ya dawo tana karbarsa kuma ta ba shi dama kamar kowa.
