Da gudunmawar Muhammad Garba na zama Shugaban NUJ na ƙasa – Kwamared Alhassan Yahaya

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano

Shugaban ƙungiyar ‘Yan Jaridu na ƙasa, Kwamared Alhassan Yahaya, ya bayyana cewa da gudunmawar Malam Muhammad Garba, tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano kuma tsohon Shugaban ƙungiyar ‘Yan Jaridu na ƙasa, NUJ kuma tsohon shugaban ƙungiyar ‘yan jaridu na Afrika WAJA yanzu kuma shugaban ma’aikata na shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Malam Muhammad Garba da gudummawarsa ne, da kuma goyan bayansa, da shawarwarin ne ta sa ya zama shugaban wannan ƙungiya na farko wanda ya fito daga Arewa maso Gabas, kuma ɗan Arewa wanda ya samu wannan muƙami bayan shekaru tara da saukar ɗan arewa a wannan lokaci. 

Saboda haka ya ce suna da kyakkyawar abun koyi daga shugabanci da mu’amala irin ta Malam Muhammad Garba kamar dai yadda shi Kwamared Alhassan Yahaya ya bayyana jim kaɗan da ɗaura auran ‘ya ga Malam Muhammad Garba da aka yi a ranar Asabar da ta gabata.

Haka kuma Kwamared Alhassan ya bayyana cewa shugabancin NUJ na ƙasa zai yi iya ƙoƙarinsa wajen ganin an inganta aikin jarida ta kowacce fuska kamar horar da ‘yan jaridu ƙwarewar aiki ta hanyar shirya kwasa-kwasai da bitoci da taron ƙarawa juna sani domin samun gogewa da ƙwarewa dai dai da zamani da kuma, albashi mai kyau, kiwon lafiya ta hanyar cin gajiyar Inshora da dai sauran duk wani abu, da doka ta yadda domin samun walwala da jin daɗin ‘yan jarida kamar yadda ya bayyana.

Haka zalika ya ce yanzu haka an samu gyare-gyare a kundin tsarin mulkin ƙungiyar ‘yan jaridu wanda kuma akwai tsare-tsare na tsarkake aikin domin inganta shi ga ahlinsa, musamman a wannan lokaci da aikin ke fuskanta ƙalubale na kasancewar barazana ga aiki da wasu dama ke ɗaukar kansu ‘yan jarida ba tare da wani horo ko wata hujja ta aiki ba da dai sauran matsaloli da NUJ ke ƙoƙarin gyarawa a Nijeriya.

A ƙarshe Kwamared Alhassan Yahaya wanda ke tare da Malam Abbas Ibrahim, mataimakin sakataren ƙungiyar ƙwadago da NLC reshen Jihar Kano ya yi wa ma’aurata nasihar riƙon gaskiya, amana, da haƙuri, tausayi domin samun kyakkyawar zuriya da za ta amfani al’umma duniya da lahira.

By ukarofi