Gwamnan Jihar Ribas ya gabatar da kasafin kuɗin 2025 ga ‘yan majalisa biyar

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Ribas Siminalayi Fubara ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2025 na naira triliyan ɗaya da biliyan ɗari takwas a gaban ‘yan majalisu guda biyar domin dubawa da kuma amincewa.

Fubara ya ce za a aiwatar da kasafin kudin shekara mai zuwa domin tabbatar da samun cigaba a tattalin arziki mai ɗorewa, da kawo cigaba ga jihar, a lokaci guda kuma zai inganta rayuwar ‘yan jihar.

Gwamnan ya ce an ware sama da biliyan 30 a fannin noma, yayin da ya ce an ware naira biliyan 63 a fannin samar da ilimi, sai kuma fannin kiwon lafiya da zai laƙumi sama da naira biliyan 97.

Kasafin kuɗin bana ya haura na bara inda aka gabatar da maira biliyan 800 a matsayin kasafin kudin 2024.

By ukarofi