Ruwa ya fi man fetur amfani wajen bunƙasa noma – Auwalu Ya’u

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano

Daya daga cikin matasa, manoma kuma ɗan kasuwa mai kamfanin sayar da injinan noma da ke Kano, Alhaji Auwalu Yau Kura, ya bayyana cewa idan aka yi amfani da dama-damai da madatsun ruwan da mu ke da su a Nijeriya wajen bunƙasa noman rani da na damina, to babu shakka za mu gane cewa arziƙi da za a samu a dalilin ruwa ya fi na man fetur amfani, musamman ma a  Kano da su ke da dama-damai, da aka samar da su sama da shekara 50 da tsohon Gwamnan Kano Alhaji Audu Bako ya samar da madatsun ruwa a zamaninsa kamar yadda ya shaida.

Ya ƙara da cewa idan gwamnatocin yanzu suka yi amfani da dama-daman wajen yanka hanyoyin ruwa da manoma za su iya amfani wajen noman rani, to za a ga alfanun abun.

Alhaji Auwalu ya cigaba da cewa, “babu shakka matsalolin rashin aikin yi, fatara, ƙarancin abinci, dogaro da kuɗin man fetur, daga gwamnatin tarayya zai zama tarihi, domin mun samu abun da ya fi shi yawa da albarka, sai dai kawai gwamnatocin mu su karɓa, domin haƙƙin al’umma ne,” inji Alhaji Auwalu Ya’u Kura, shugaban kamfanin African Farm Machinery.

Haka zalika ya ƙara da cewa “Kano, Arewa baki ɗaya Allah, ya albarka ce ta ƙasa mai kyau da duk abin da a ka noma zai yi, kamar a nan Kano, irin su ƙaraye sun fara jarraba abarba kuma ta na yi da sauran gurare a Kano da Arewa duk ana shuka komai, irinsu tufa, ayaba, da sauran kayan marmari da abinci duk babu wanda ba ya yi a wannan yanki namu.

“Saboda haka akwai buƙatar Shugaban ƙasa Alhaji Ahmad Bola Tinubu, da gwamnan mu na Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da sauran gwamnoni, su ba da himma wajen ganin an wadata manoma da kayan aiki na zamani wanda zai kawar da matsalolin da mu ke ciki na tsadar abinci wanda ƙarancinsa ne ke kawo tsada kamar yadda abin ya ke a ilimance.”

By ukarofi