Fafaroma ya sake bai wa ɗan Nijeriya babban muƙami a Fadar Vatican

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Fafaroma Leo ya naɗa Monsignor Anthony Onyemuche Ekpo a matsayin sabon Mai Kula da Harkokin Yau Da Kullum (Assessor for General Affairs) a Ma’aikatar Harkokin ƙetare ta fadar Vatican, wani babban matsayi da ke ƙara wa Nijeriya daraja a cikin Cocin Katolika ta duniya.

Kafin wannan naɗin, Ekpo yana aiki a matsayin Mataimakin Sakataren Ma’aikatar Inganta Ci Gaban Bil’adama. Firist ne daga Diocese na Umuahia, an haife shi a Umudike a ranar 24 ga Satumba, 1981 kuma an naɗa shi firista a ranar 30 ga Yuli, 2011.

Wannan shi ne karo na biyu cikin watan nan da Fafaroma Leo ke ba ɗan Nijeriya babban muƙami a fadar Vatican.

A makon da ya gabata ne Fafaroma ya naɗa Fr. Edward Daleng daga Jihar Filato a matsayin Mataimakin Shugaban Ofishin Kulawa da Ayyukan Fafaroma da ba na Ibada ba (Vice Regent of the Prefecture of the Pontifical Household).

Ekpo na da digiri a fannin tsarin addini (systematic theology) da kuma dokokin cocin Katolika (canon law). Ya fara aiki da fadar Vatican a ranar 5 ga Satumba, 2016 a sashen Harkokin Gabadaya, kuma daga bisani aka naɗa shi a matsayin Mataimakin Sakataren Ma’aikatar Inganta Ci Gaban Bil’adama a ranar 18 ga Afrilu, 2023.

By ukarofi