
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta sanar da umarnin rufe makarantunta na sakandare na kwalejojin tarayya da ake kira da ‘Unity Colleges’ da ke sassan arewacin Nijeriya.
A sanarwar da Ma’aikatar Ilimi ta fitar a ranar Juma’a daga Daraktar makarantun sakandare, Binta Abdulqadir a madadin Ministan Ilimi, Tunji Alausa, gwamnatin ta sanar a rufe kwalejojin guda 41 a faɗin Nijeriya.
Sanarwar ta ce, ma’aikatar ta ɗauki wannan matakin ne saboda barazanar tsaro da ake fuskanta a sassan ƙasar, da kuma yunƙurin daƙile afkawa cikin wata matsala.
Sanarwar ta kuma umarci shugabannin makarantun su tabbatar an aiwatar da umarnin a nan take ba tare da wani jinkiri ba.
Ga jerin kwalejojin da aka rufe daga jihohi daban-daban a arewacin Nijeriya:
- FGGC MINJIBIR
- FTC GANDUJE
- FGGC ZARIA
- FTC KAFANCHAN
- FGGC BAKORI
- FTC DAYI
- FGC DAURA
- FGGC TAMBUWAL
- FSC SOKOTO
- FTC WURNO
- FGC GUSAU
- FGC ANKA
- FGGC GWANDU
- FGC BIRNIN YAURI
- FTC ZURU
- FGGC KAZAURE
- FGC KIYAWA
- FTC HADEJIA
- FGGC BIDA
- FGC NEW-BUSSA
- FTC KUTA-SHIRORO
- FGA SULEJA
- FGC ILORIN
- FGGC OMUARAN
- FTC GWANARA
- FGC UGWOLAWO
- FGGC KABBA
- FTC OGUGU
- FGGC BWARI
- FGC RUBOCHI
- FGGC ABAJI
- FGGC POTISKUM
- FGC BUNI YADI
- FTC GASHUA
- FTC MICHIKA
- FGC GANYE
- FGC AZARE
- FTC MISAU
- FGGC BAJOGA
- FGC BILLIRI
- FTC ZAMBUK
Hakan na zuwa ne yayin da al’amarin taɓarɓarewar tsaro ya yi ƙamari a sassan ƙasar duba da yadda ake cigaba da yin awon-gaba da ɗalibai a makarantu.
A wani labarin kuma, rundunar ƴan sandan jihar Nasarawa ta ce rahton garkuwa da ɗalibai guda biyu na makarantar St. Peter’s Academy da ke Doma ba gaskiya ba ne.
