Shettima zai wakilci Tinubu a taron G20

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A jiya Juma’a Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya bar Abuja domin wakiltar Shugaba Bola Tinubu a babban taron shugabannin ƙasashe na G20, wanda za a yi Johannesburg na ƙasar Afirka ta Kudu.

Da fari Shugaba Tinubu ya tsayar da tafiyarsa ta Johannesburg ne domin jin ba’asin lamuran tsaro da ya shafi jihohin Kebbi da Kwara, inda aka yi garkuwa da ɗalibai da masu ibada.

Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu, wanda shi ne shugaban G20, ya gayyaci takwaran nasa na Nijeriya domin halartar taron na wannan shekarar.

A yau 22 ga Nuwamba da gobe 23 ga wata za a gudanar da taron, wanda zai haɗa manyan ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziƙi ciki har da Ƙungiyar Tarayya Turai (EU), Ƙungiyar Afirka (AU) da cibiyoyin kuɗi da sauran su.

Tun da farko Tinubu ya dakatar da tafiyarsa ta G20 da taron AU-EU a Luanda, Angola.

Kakakin Shugaban Ƙasa Bayo Onanuga ya sanar da hukuncin tun a ranar 19 ga Nuwamba, inda a yayin haka ne kuma Shugaban Ƙasar ya umarci rundunonin sojoji da ƴan sanda da su tura ƙarin wasu jami’ai zuwa Kwara.

Ya kuma bada misali da aukuwar hare-hare da garkuwa da mutane, waɗanda a cewarsa suna faruwa ne sakamakon rashin kasancewar shugaban ƙasar a Nijeriya.

Tinubu ya umarci ƙarin jami’an tsaro ne bisa ga buƙatar da Gwamnan Kwara ya gabatar masa, wanda ake ganin zai taimaka wa ƙoƙarin jami’an na atisayen ceto mutanen.

Sannan ya umarci ƴan sanda da su ruɓanya ƙoƙarinsu wajen ganin sun kamo ƴan bindigar da ke da hannu a hare-haren.

By Babaji