Matsalar Tsaro: Rundunar sojojin Nijeriya ta nemi ‘yan jarida su riƙa tantance rahotanninsu

Spread the love

Daga HABU ƊAN SARKI, Jos

Sashin hulɗa da jama’a na hedkwatar rundunar sojojin ƙasa ta Nijeriya ya shiryawa manema labarai wani taron bita game da muhimmancin tantance bayanan da za a yaɗa ga jama’a, musamman wanda ya shafi tsaron rayuwar al’umma a ƙasar nan.

Taron wanda ya gudana a Jos, ya samu halartar Babban Hafsan Sojojin Nijeriya, Laftanar Janar Waheed Shaibu, da wasu manyan jami’an tsaro, da shugabannin kafafen watsa labarai, ciki har da Babban Daraktan NTA Salihu Abdulhamid Dembos.

Manazarta harkokin tsaro a taron sun koka da yadda cigaban da ake samu a fasahar sadarwa ke haifar da ƙarin matsalolin tsaro, musamman a ɓangaren yaɗa labaran ƙarya, jita-jita, da yaɗa farfaganda. Sau da dama, manema labarai ma na iya faɗawa cikin tarkon masu yaɗa labaran ƙarya ko karkatar da gaskiyar labari, yayin da hakan ke iya zama barazana ga zaman lafiyar al’umma da cigaban tsaro.

An yi kira ga manema labarai su riƙa tantance rahotannin da suke samu, da tabbatar da ingancin tushen da suka samu labari, tare da riƙo da ƙa’idojin aikin jarida sau da ƙafa.

Manema labarai da suka samu halartar taron sun yi alƙawarin amfani da darussan da aka koya musu, da kiyaye dokokin da aka tantance labari, don kaucewa samun matsala cikin al’umma.

By ukarofi