
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Bisa la’akari da hukuncin Babbar Kotun Tarayya ta Abuja, Hukumar Tsaro ta Farin kaya (DSS), ta kai tsararren jagoran ƙungiyar fafutukar kafa ƙasar Biafara (IPOB), Nnamdi Kanu zuwa gidan gyaran hali a Jihar Sakkwato.
Wata majiya daga hukumar ta shaida wa manema labarai cewa an ɗauki matakin ne bayan yanke masa hukuncin ɗaurin rai-da-rai da kotu ta yi bisa samunsa da hannu a laifuka bakwai masu alaƙa da ta’addanci.
Da yake gabatar da shari’ar a ranar Alhamis a Abuja, Alƙali James Omotosho ya umarci DSS ta mayar da Kanu zuwa kowane kurkuku a ƙasar banda na Kuje a Abuja.
Mai shari’a Omotosho ya bayyana cewa zarge-zargen da hukumar DSS ta shigar akan jagoran ƴan tawaren na IPOB sun haddasa ta’addanci na kiran da yake yi akan a ware yankin Kudu maso Gabas, jihohin kudu da wasu sassan jihohin Benuwai da Kogi daga Nijeriya.
Haka ma Lauyan Kanu, Aloy Ejimkor, wanda shi ma ya tabbatar da sauya wa Kanu gidan yari a wani rubutu ta kafar X, ranar Juma’a.
Ejimkor ya koka game da matakin inda ya ce sauya gidajen yari ga Kanu zai nesanta shi da tawagar lauyoyinsa, iyalai da magoya baya, yana mai ƙalubalantar hakan.
A shekarar 2015 ne hukumomin tsaron Nijeriya suka fara kama Kanu inda ya fuskanci tuhumar cin amanar ƙasa, ta’addanci da wasu laifuka masu kama da haka. Sannan aka sake kama shi a Kenya a shekarar 2021.
