CAN ta tabbatar da garkuwa da ɗalibai 215 da ma’aikata 12 a harin makarantar Neja

Spread the love

Ƙungiyar Kiristocin Nijeriya (CAN), ta ce kimamin mutune 227 da suka ƙunshi ɗalibai 215 da malamai 12 ƴan bindiga suka yi awon-gaba da su a lokacin da suka kai hari makarantar St. Mary da ke garin Papiri a Jihar Neja.

A wata sanarwa da shugaban ƙungiyar reshen jihar, Most Rev. Bulus Dauwa Yohanna ya fitar, ya ce harin ya jefa al’ummar yankin cikin ɗimuwa da firgici.

Da tsakar daren ranar Alhamis ne wasu mahara ɗauke da muggan makamai suka far wa makarantar wadda ta kwana ce, da ta ƙunshi firamare da sakandire, inda suka sace ɗaliban, bayan sun harbi maigadi.

Tuni gwamnatin jihar ta ce sai da bayar da umarnin rufe duka makarantun yankin sakamakon samun bayanan sirri kan barazanar tsaro, amma makarantar ta yi gaban kanta wajen buɗewa tare da cigaba da gudanar da harkokin karatu ba tare da neman izini ko sanar da ita ba.

Wannan hari na zuwa ne ƙasa da mako guda da wasu ƴan bidiga suka yi garkuwa da ɗalibai mata 25 a makarantar sakandiren ƴan mata da ke garin Maga a Ƙaramar Hukumar Danko-Wasagu na Jihar Kebbi.

Akan haka ne Gwamnatin Tarayya ta sanar da baza ƙarin jami’an tsaro domin kuɓutar da duka ɗaliban kamar yadda Bayo Onanuga, Kakakin Shugaban ƙasa ya bayyana.

By Babaji