
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gamayyar Ƙungiyar masu Shirya Fina-finai ta ƙasa (MOPPAN) ta miƙa saƙon jajentawa ga gwamnati da al’ummar jihar Kebbi, bisa awon-gaba da ƴan bindiga suka yi da ɗalibai mata guda 25 a makarantar Government Comprehensive Girls’ Secondary School, Maga da ke jihar a farkon makon da ya gabata.
Shugaban ƙungiyar, Shehu Hassan Kano ya sanar da haka a wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Sakataren MOPPAN, Dakta Mohammed Ibrahim Gumel, ranar Juma’a.
Ya ce, “Masana’antar Kannywood ta shiga ɗimuwa da tadhin hankali bisa wannan mummunan iftila’i da ya faru. Allah ya kiyaye, Allah ya hana faruwar haka a nan gaba.”
Ƙungiyar ta kuma ce, tana fatan Shugaba Bola Tinubu da Mai ba shi shawara akan harkar tsaro Malam Nuhu Ribaɗu za su yi abinda ya dace wajen ganin an ceto ɗaliban.
Haka kuma, “MOPPAN na taya su addu’a da fatan alkhairi. Allah ya kwantar da hankalin al’ummar arewacin Nijeriya da ma Nijeriya baki ɗaya.”

