Daga BELLO HAMZA
Kimanin watanni 10 ke nan da za a fara aiwatar da tsare-tsaren da za su kai ga zaɓuka masu zuwa a faɗin ƙasar nan, masana harkokin siyasa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar adawa ta PDP, suna ta faɗi tashin ganin wa zai iya kokawa da kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Bayan shan kaye a jere a zaɓukan shugaban ƙasa har guda uku, PDP na neman sabuwar hanyar da za ta taka ta kai ta ga nasara a 2027.
Wasu masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar PDP, kamar yadda wani masanin tarihin ƙasar Amurka, Allan Lichtman, wanda ya yi suna wajen yin hasashe guda tara daga cikin 10 na zaɓen shugaban ƙasa na baya-bayan nan da aka yi a ƙasar Amurka, sun ce sun yi na’am da gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, a matsayin wanda zai iya lashe tikitin takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar a 2027.
Duk da cewa yunƙurin Makinde na neman shugabancin ƙasar ya ci gaba da zama hasashe ne, amma alamu na nuni da cewa ba wasu tsiraru ne a jam’iyyar ba ne suka amince da ƙarfin tikitin Makinde.
A yayin da al’ummar ƙasar ke cikin mawuyacin hali, sakamakon taɓarɓarewar farashin man fetur, ƙarin kuɗin wutar lantarki, da faɗuwar darajar Naira, ‘yan Nijeriya na sake fahimtar kaifin sakamakon zaɓen 2023, wanda ya sanya jam’iyyar APC ta ci gaba da kasancewar a kan mulki.
A don haka, kwaɗayin samun canjin shugabanci a matakin ƙasa ya haifar da ƙwarin gwiwa wajen ganin an gina tubalin da zai kai mu zuwa shekarar 2027, wanda aikin da ake yi na samar da tsarin siyasa ba zai wadatar kaɗai ba idan ba a gabatar da wani babban dan takara ba mai nagarta ba.
Duk da rigingimun cikin gida da ke cikin jam’iyyar PDP, wasu masu ruwa da tsaki sun haƙiƙance a kan cewa hanyar da jam’iyyar za ta bi wajen samun nasara a zaɓen 2027 shi ne ta tsayar da dan kasuwan nan kuma dan asalin Jihar Oyo wanda ya kasance ɗan siyasa ne a matsayin dan takararta wanda shi ne zai kayar da zaɓin APC na kai tsaye na Shugaba Bola Tinubu.
Ga manyan masu ruwa da tsaki da suke da wannan ra’ayi, sun ce Gwamna Makinde yana da kwarjini da kuma tsarin da zai kai PDP ga samun nasara a 2027.
Ba kamar yadda jam’iyyar PDP ta zaɓi ɗan takarar Arewa a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ba, masana da masu ruwa da tsaki na ganin cewa ya kamata ɗan takarar kudancin ƙasar ya daga tutar jam’iyyar a 2027.
A cewarsu, wannan matakin zai warkar da raunukan da ‘yan kudancin ƙasarnan suka samu sakamakon fitar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar a matsayin wanda ya lashe tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a 2023.
Bisa haka ne, a kwanakin baya wasu masu ruwa da tsaki suka fara yaƙin neman ganin Makinde ya tsaya takarar shugaban ƙasa a shekarar 2027.
ƙungiyar da ke ƙarƙashin inuwar ‘Progressiɓe Youth for Makinde Presidency 2027’ a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, ta bayyana cewa, Makinde ya nuna nagartattun halaye na shugabanci da jajircewa wajen gudanar da shugabanci na gari, wanda hakan ya sa ya dace da shugabancin Nijeriya.
ƙungiyar ta fara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na 2027 na Makinde ne a watan Yunin wannan shekara. Duk da cewa yaƙin neman zaɓen na Makinde 2027 ya takaita ne a shafukan sada zumunta, saƙon na su ya yi daidai da kyakkyawan jagoranci na Gwamnan Jihar Oyo.
Wani fitaccen mai goyon bayan Makinde, Olamilekan Kehinde, wanda bai ɓoye yunkurinsa na ganin gwamnan ya tsaya takara a zaɓen shugaban kasa a 2027 ba, ya bayyana ƙwarin guiwarsa kan Makinde, inda ya ce Makinde ya nuna nagartattun halaye na shugabanci da jajircewa wajen gudanar da shugabanci nagari, wanda hakan ya sa ya dace da shugabancin Nijeriya idan aka kwatanta da shugabancin ƙasar a yanzu.
Da yake tabbatar da hakan, ƙungiyar ‘Oyo Renaissance Group’, ta bayyana Makinde a matsayin mutum mai jajircewa a jam’iyyar wanda bai taba watsi da manufa da muradin jam’iyyar PDP ba.
Kodinetan ƙungiyar Kwamared Dayo Adedoyin, a wata sanarwa da ya fitar a baya-bayan nan, ya ce, “Gwamna Makinde ya nuna halayensa na jagoranci da kuma ƙwazonsa wajen cika alƙawuran da ya yi wa al’ummarsa a jihar Oyo a cikin jerin ayyuka da manufofin da ya dace ga al’umma wanda ya ɗauki lokaci yana gudanarwa a matsayinsa na gwamnan Jihar Oyo daga 2019 zuwa yau.
“Gwamna Makinde ya tsayu kyam wajen tafiyar da jam’iyyar kuma zai ci gaba dayin aiki tare da takwarorinsa gwamnonin da aka zaba a jam’iyyar PDP a jihohi daban-daban na tarayya ta hanyar aiwatar da manufofi da tsarin jam’iyyar.”
Bincike ya nuna cewa Makinde bai taɓa gujewa zama ɗan cikakken dan jam’iyya ba. Har wala yau bincike ya nuna cewa gwamnan tun bayan hawansa mulki a shekarar 2019, ya ci gaba da tallafa wa ma’aikatan PDP a Sakatariyyar jam’iyyar na ƙasa, da kuma Kwamitin Ayyuka na Jam’iyyar (NWC) da Hukumar Amintattu (BoT).
Shi kaɗai ne ya ba da kuɗi wajen gina sabon ofishin Cibiyar Dimokuradiyyar Al’umma mai suna ‘Peoples Democratic Institute (PDI)’, wanda cibiya ce ta zurfafa tunani na jam’iyyar, aikin da ya laƙume daruruwan miliyoyin naira.
Domin ci gaba da nuna jajircewarsa na ci gaban jam’iyyar ba tare da wata tangarɗa ba, Makinde ya gina Sakatariyar jam’iyyar PDP shiyyar Kudu maso Yamma a Ibadan tare da sanya mata sunan shugaban jam’iyyar, Hon. Soji Adagunodo wanda ya rasu yana kan mulki. Za a ƙaddamar da ginin nan ba da jimawa ba.
A baya-bayan nan ne ya biya dukkan ma’aikatan sakatariyar jam’iyyar PDP na ƙasa alawus-alawus ɗin gidaje da suka haɗa da masu taimaka wa jam’iyyar na NWC da kudi kusan Naira miliyan 300.
Da yake tantance yiwuwar nasarar jam’iyyar PDP a 2027, manazarci kan al’amuran al’umma kuma shugaban ƙungiyar ‘Reset Lagos PDP’, Dakta Adetokunbo Pearse, ya tabbatar da cewa, PDP na da kyakkyawar damar ɗarewa kan kujerar shugabancin ƙasa a 2027 duk da rikicin cikin gida da yake cikin jam’iyyar. Ya kuma yi imanin cewa damar jam’iyyar zai kai gaci ne idan aka bai wa Makinde dama a matsayin ɗan takara.
“Masu sharhin siyasa da ke tunanin cewa akwai matsalar shugabanci a PDP sun yi kuskure sosai. Mukaman shugabanci a dukkan matakai na jam’iyyar yana nan a yadda yake. Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar daɗaɗɗe, Sanata Wabara shi ne shugaban kwamitin amintattu (BoT), Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP, kuma Ambasada Umar Iliya Damagum shi ne shugaban riƙo na ƙasa na jam’iyyar,” in ji Pearse.
Pearse, wanda tsohon memba ne na Majalisar Kamfen din Shugaban ƙasa na PDP a 2023, ya ci gaba da cewa, sabanin ra’ayin da ake yaɗawa al’umma, PDP ba ta tsayar da tikitin takarar shugaban ƙasa ba tun da babu wani daga kowanne yanki na siyasa da aka hana shi shiga zaɓen fidda gwani na jam’iyyar. Abin da ke tabbatar da shiyyar shugaban ƙasa shi ne samar da shugaban jam’iyya.
Ya ce ga dukkan alamu mukamin shugabacin jam’iyya zai ci gaba da zama a Arewa ne kuma tikitin takarar shugaban ƙasa zai koma Kudu.
Dangane da ra’ayin cewa Gwamna Makinde ne zai kasance a matsayin ɗan takarar jam’iyyar a shekarar 2027, Dakta Pearse ya ce ana kallon Makinde a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a 2027.
“Ina ganin wannan hasashe ya samo asali ne daga yadda Makinde ya yi fice a matsayinsa na Gwamnan Jihar Oyo, da kyawawan halayensa, da jajircewarsa ga dimokuradiyya, da bin doka da oda. Yana gudanar da mulki ta hanyar sanya kowa da kowa. An gaya mini cewa ana kiransa “Seyi Masoyi.”
“Idan Makinde ya lashe zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na PDP kuma ya fito a matsayin dan takarar jam’iyyar, zai zama shugaban Nijeriya a 2027,” in ji Pearse.
Ya kuma bayyana cewa Nijeriya na buƙatar sauya alƙibla daga gwamnatin APC mai cike da ruɗani. “Ba wata jam’iyyar siyasa da take tsarkakakkiya, amma idan aka kwatanta da APC, PDP mai daraja ce,” in ji Pearse.
Shi ma mataimakin sakataren yaɗa labaran jam’iyyar PDP na ƙasa Dr. Ibrahim Abdullahi yana da wannan ra’ayin. Kuma yana ganin Makinde zai iya zama dan siyasar PDP da za a fafata da shi.
A nasa jawabin, Abdullahi ya ce damar PDP a 2027 ya fi kowanne irin lokaci saboda rashin aikin da Tinubu da gwamnatin APC ke yi, wanda ke ci gaba da jawo wahalhalu da bacin rai a ƙasar nan.
“Idan aka yi la’akari da yadda al’amura ke gudana, za a iya mayar da takarar shugabancin ƙasarnan a 2027 zuwa Kudu-maso-Yamma cikin dabarar da PDP za ta iya cimma a tare bisa kyakkyawar cimma matsaya ta ‘yan Arewa kan wanda zai zama abokin takarar. Wannan domin gamsar da ra’ayoyin Kudu game da ƙididdigar yanki da addini bisa lura da yadda Tinubu ya amfana da wannan rarrabuwar.
“Da ma gwamna Seyi Makinde ya yi daidai da ainihin abin da PDP ke buƙata a lissafin tikitin takarar shugaban ƙasa a 2027.
Sai dai kuma wani abin ban mamaki shi ne, har yanzu gwamnan bai nuna sha’awa ba, domin ga dukkan alamu ya shagaltu da ayyukan al’umma domin bunƙasa zamantakewa da tattalin arzikinsu.
Yana daya daga cikin jiga-jigan gwamna mai aikin a zo a gani a wannan jamhuriyya. Ana auna shi a matsayin wanda yake da babbar dama wajen jan wannan ragama.
“ƙasar nan tana cikin halin rugujewa da baganniya, tir da halin gwamnatin APC mara basira. Ya bayyana cewa suna kan turbar tukin da babu direba. Taɓarɓarewar hauhawar farashin kayayyaki yana haɗe ne da gazawar gudanarwa wajen mayar da Nijeriya kasa mafi muni a doron ƙasa wajen gudanar da rayuwa a cikinta,” in ji Abdullahi.
Sai dai Makinde ba bakon ba ne wajen shawo kan taƙaddamar siyasa kamar yadda ya yi a 2019, lokacin da ya kayar da ikon da ke jihar Oyo ya lashe zaɓen gwamna.
Jam’iyyar PDP a jihar Oyo kafin 2019 ta kwanta dama. Gabanin zaɓen 2019, babban jigon jam’iyyar, tsohon Gwamna Rashidi Ladoja, ya jefar da jam’iyyar ya koma jam’iyyar Accord Party saboda bai ji daɗin yadda aka raba tsarin jam’iyyar ba.
Wata majiya mai tushe a siyasar jihar Oyo ta ce, “Na tuna a lokacin hatta dan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi kakkausar suka ga Ladoja da ya fice daga jam’iyyar, har ya kai ga shi (Atiku) ya kira Sakataren tsare-tsare na ƙasa na jam’iyyar a lokacin, Kanal Austin Akobundu mai ritaya (yanzu Sanata ne), da kuma shugaban jam’iyyar na lokacin, Prince Uche Secondus, cewa babu wani dalilin da zai sa Ladoja ya fice daga jam’iyyar.
“Ladoja ya bar jam’iyyar ne saura ‘yan watanni kafin zaɓen 2019, kuma wanda ya rage (cikin masu ruwa da tsaki) shi ne dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Seyi Makinde.
“Sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na 2019 ya nuna cewa PDP ta lashe jihar ga Atiku, kuma Seyi Makinde ne ya ci zaɓen gwamna da tazara mai yawa.
“Eh, kowa na iya cin zaɓe, amma maganar gaskiya, a Jihar Oyo a lokacin, Makinde ne ya yi ruwa ya yi tsaki, ya yaki gwamnati mai ci, tsofaffin gwamnonin biyu (Ladoja da Marigayi Alao Akala) waɗanda dukkansu ke da bambancin ra’ayi, minista mai ci, kuma mafi muhimmanci, Gwamnatin Tarayya ta APC a tsakiya.
“Ya yi ƙoƙari ya iya ƙwace taura a hannun kuturu domin al’umma, sannan ƙarfin ikon Allah yana tare da shi. Kafin shekarar 2019, Jam’iyyar ba ta da wakilci a dukkan faɗin ƙasa, amma a zaɓen 2019, PDP ta lashe kujerun Gwamna, da Sanata, da kujeru biyar na Majalisar Tarayya, duk waɗannan daga Jam’iyyar da aka yi wa laƙabi da matattu,” inji majiyar. .
A yayin da PDP ke neman sabuwar alƙibla kafin 2027, shin Makinde, wanda aka fi sani da tauraro mai haske na wato ‘PDP Star-Boy’ a turance, zai iya maimaita tarihi ta hanyar yin galaba a kan duk wani ƙalubale wajen kasancewa a matsayin dan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar? Amsar tana cikin watanni masu zuwa.
Malam Bello shine Mataimakin Editan Jaridar LEADERSHIP HAUSA da ake wallafawa a Abuja, Babban Birnin Tarayyar Nijeriya
