Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Farashin kayan abinci ya sauka warwas a jihohin Borno, Yobe da Adamawa, a cewar binciken da Hukumar Labarai ta Nijeriya (NAN) ta gudanar.
Binciken NAN da aka yi a manyan kasuwanni a Maiduguri, Damaturu, Yola ta Arewa da Numan ya nuna raguwar farashin shinkafa, masara, wake, barkono, gero, taliya da man gyaɗa idan aka kwatanta da farashin farkon shekarar.
A Kasuwar Litinin da ke Maiduguri, buhun shinkafa mai kilo 50 da aka sayar a tsakanin N78,000 zuwa N82,000 a watan Agusta da Satumba, yanzu tana sayarwa tsakanin N64,000 zuwa N65,000.
Haka zalika, buhun masara mai kilo 100 da farashinta ya kasance tsakanin N60,000 zuwa N65,000 yanzu tana sayarwa tsakanin N40,000 zuwa N45,000. Wake fara da aka sayar a matsakaici N105,000 yanzu ya sauka zuwa N85,000, yayin da kwandon barkono wanda ya kai N70,000 zuwa N85,000 a lokacin ƙarancin sa, yanzu yana tsakanin N6,500 zuwa N8,500.
Haka kuma, buhun gero kilo 100 yanzu ana sayarwa kusan N46,000, daga N65,000 da aka sayar watanni uku da suka wuce. Masara irin sorghum ta kuma sauka zuwa kusan N38,000 daga N50,000 zuwa N55,000.
Malam Haruna Bukar, ɗan kasuwa a kasuwar, ya danganta raguwar farashin da ƙaruwar samuwar kayayyaki daga manoma na cikin gida da kuma samun sauƙin zuwa gonaki, sakamakon kyakkyawan yanayin tsaro a wasu sassan Jere, Konduga da Mafa.
Hajiya Amina Umar, mai sayar da wake da garri, ta bayyana cewa wannan sauƙin farashin abin maraba ne, amma tana gargaɗin cewa zai iya kasancewa na ɗan lokaci.
Ta ce, “Abokan ciniki suna farin ciki, amma mu ‘yan kasuwa muna fargabar farashin zai tashi idan wannan girbin ya ƙare saboda rashin ajiyar kaya. Idan gwamnati ta samar da cibiyoyin ajiya, za mu iya saye da yawa mu kiyaye farashin ya tsaya.”
Fatima Mohammed, mai sayar da barkono, ta ce raguwar farashin barkono ya biyo bayan samun girbin kayan daga gonaki a Biu, Shani da Damboa.
Ta kuma jaddada cewa hauhawar farashin kayan da za a iya lalacewa na da nasaba da tsadar sufuri.
Malam Babagana Lawan, mai sayar da sorghum da gero a Kasuwar Tashan Bama, ya ce rashin tsaro da tsadar sufuri sune manyan barazanar da ke hana daidaiton farashin.
Dekta Binta Yahaya, masanin tattalin arziki daga Jami’ar Jihar Yobe, ta ce raguwar farashin ya samo asali ne daga shigo da hatsi da yawa da gwamnatin yanzu ke yi, wanda ya sa kasuwanni suka cika da kaya, hakan ya tilasta wa farashin sauka.
Yahaya ta shawarci gwamnati ta aiwatar da matakan da za su tallafa wa manoma wajen samun kayan aikin gona da takin zamani da araha, domin farashin ya ci gaba da kasancewa a matakin da ya dace ba tare da cutar da manoma ba.
A Kasuwar Yola, buhun shinkafa kilo 50 yanzu tana siyarwa tsakanin N32,000 zuwa N36,000, daga N48,000 zuwa N55,000 watanni uku da suka wuce. Masara matsakaici yanzu tana siyarwa tsakanin N550 zuwa N650, daga N1,000 a farkon shekara. Wake matsakaici ya sauka daga N1,500 zuwa kusan N900 zuwa N1,000.
Masu sayarwa da abokan ciniki sun jaddada buƙatar gwamnatin tarayya da ta jihohi ta tallafa wa manoma da tsarin sufuri da ajiyar kaya, domin tabbatar da cewa sauƙin farashi ya ɗore a tsawon lokaci.
