Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon ɗan majalisar wakilai, Farouk Lawan, wanda aka yanke wa hukunci saboda samunsa da laifin cin hanci da rashawa ya shaƙi iskar ‘yanci bayan shafe shekaru biyar a gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja.
Tsohon ɗan majalisar ya wakilci Bagwai/Shannon a majalisar wakilai daga Kano a shekarun 1999 to 2015.
A cikin wani jawabi da ya sanya wa hannu a ranar Talata, Lawan, ya bayyana cewa Allah ya yi masa fitowa bayan kammala wa’adin da kotu ta ɗibar masa tare da miƙa godiyarsa ga Allah bisa samun damar buɗe sabon shafi a rayuwarsa.
Ya kuma ce yana cikin ƙoshin lafiya, inda ya gode wa iyalansa da abokai da sauran abokan arziƙi kan gudunmawar da suka ba shi a lokacin da yake ɗaure.
Zuwa yanzu dai Manhaja ba ta kai ga tantance ainihin lokacin da ya fita daga gidan yarin ba.
Lawan fitaccen ɗan majalisar tarayya ne da ya riƙe shugaban kwamitin na wucin gadi wanda aka ɗora wa alhakin binciken wata badaƙalar kuɗin tallafin man fetur a lokacin shugabancin tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan a shekarar 2012.
A wancan lokaci ana yi masa take ne da mai gaskiya saboda irin tsarin aƙidar da yake da ita na yaƙi da cin hanci da rashawa.
Cikin rahoton kwamitin da ya jagoranta, ya zargi kamofnin Zenon Oil da karɓar canjin Dala har Dala miliyan 230 daga babban bankin Nijeriya da sunan tallafin man fetur domin kawo mai amma sai kamfanin ya gaza yin hakan.
Sai dai daga baya, ya cire sunan kamfanin daga jirin kamfanonin da yake bincike a kansu bayan karɓar cin hanci na Dalar Amurka 500,000 daga Mista Otedola a matsayin wani ɓangare na Dala miliyan 3 da aka yi masa alƙawari.
Sai dai duk mutanen biyu da mai bayarwa da mai karɓa sun ce sun yi haka ne domin kama ɗayensu da laifin cin hanci da rashawa.
Sai dai mista Otedola ya tabbatar da cewa ya sanar da hukumar yan sandan farin kaya ta SSS kan yunƙurin ƙoƙubarsa kuɗi da Lawan ke shirin yi ba tare da hujja ba.
Inda ɗan kasuwar ya ce hukumar ce ta ce ya yi abin da ya yi kuma har aka kai ga kama shi a wani faifan bidiyo a lokacin da yake karɓar kuɗin.
Sai dai shi a nasa ɓangeren Lawan ya nuna cewa ya karɓi kuɗin ne domin ya zama hujja a kan mista Otedola na yunƙurin ba shi cin hanci.
Sai dai ofishin babban mai shari’a na ƙasa ta hannun babban lauya, Adegboyega Awomolo, ta same tsohon ɗan majalisar da laifi da ya saɓa wa sashe na 18(1)(a) na kundin laifuka da suka shafi cin hanci da sauran laifuka makamantansa da kuma laifin da ya saɓawa sashe na 17(1)(a) na shekarar 2000.
A yayin da take yanke hukunci a ranar 22 ga watan Yunin 2021, mai shari’a, Angela Otaluka, ta babbar kotun Abuja ta yanke wa tsohon ɗan majalisar hukunci kan laifuka guda uku.
Sai dai kotun ɗaukaka ƙara a watan Fabarairun 2022 ta wanke shi daga laifuka biyu, inda ta kama shi da guda ɗaya wanda da fari kotun ta ɗaure shi na tsawon shekaru 7 kafin daga bisani ta rage masa 2 zuwa zaman shekaru 5.
