Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya ce kawo yanzu tun da ya hau karagar mulki a matsayin gwamnan jihar daga shekarar 2019 zuwa 2024 da ake ciki gwamnatinsa ta ci ribar sama da zunzurutun kuɗi har Naira biliyan 1 daga hukumar nan dake tattara bayyanan filaye da sauran kaddarorin al’ummar jihar wadda ake kira Nasarawa Geographic Information System NAGIS a Turance.
Gwamnan ya sanar da haka ne a jawabinsa a wajen bikin sake buɗe babban ofishin hukumar ta NAGIS wadda ya ci wuta sakamakon wani gobara da ya auku kwanakin baya a babban ofishin tare da bikin ƙaddamar da makon kwastamomin NAGIS ɗin na shekarar 2024 da ake ciki wadda aka gudanar a Lafiya babbar birnin jihar ranar Talata.
Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana cewa tun zuwansa ya yanke shawarar cigaba da tallafa wa hukumar don bunƙasar ta don cimma burin kafuwar ta inda ya kuma yaba wa hangen nesa da wanda ya fara kafa hukumar wato tsohon gwamnan jihar Sanata Umaru Tanko Almakura da Darakta Janar na hukumar Sunny Agassi dangane da kafa hukumar dake da manufar samowa gwamnati kuɗaɗen shiga tare da samar wa masu mallakan filaye da sauran kaddarori ingantattun takardun mallakar dukiyar nasu da sauransu, inda ya yi alƙawarin cigaba da tallafa wa hukumar kana ya buƙaci al’ummar jihar baki ɗaya su riƙa ziyartar hukumar don cin moriyarta.
Shi ma da yake jawabi maimartaba Sarkin Nasarawa a jihar Alhaji Ibrahim Jibrin ya jinjina wa Gwamna Abdullahi Sule ne dangane da samar wa hukumar tallafin akai-akai wanda hakan nesa a cewarsa ya sa kuɗaɗen shigar gwamnatinsa ke cigaba da ƙaruwa musamman wanda ake samu daga hukumar ta NAGIS inda ya buƙaci gwamnan ya cigaba da wannan kyawawan aiki.
Tun farko a jawabinsa na maraba babban daraktan janar na hukumar ta NAGIS a jihar Sunny Agassi bayan ya marafci duka baki da suka samu damar hallarar bikin ya kuma yaba wa gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule game da taimako da tallafi na musamman da yake bai wa hukumar akai-akai don samun cigaba da bunkasar harkokin ta akoyaushe inda ya ta’alakanta duka nasarorin da hukumar ta cimma kawo yanzu wa ƙoƙarin na gwamnatin Injiniya Abdullahi Sule musamman tallafin da ya bayar a lokacin da babban ofishin nasu dake Lafiya ɗin ya kama da wuta da dai sauransu.
A ƙarshe wakilinmu dai ya gano cewa jim kaɗan bayan aukuwar gobarar da ya yi sanadiyyar ƙona masu muhimman kaddarorin hukumar ta NAGIS ne sai Gwamna Sule ya bada umurnin sake gyara inda a yanzu da aka kammala aka sake bikin buɗe shi.
