Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Tirelar mai ɗauke da siminti mallakin kamfanin siminti na BUA Sokoto ta taka wani abu mai fashewa da ake zargin ‘yan ta’adda suka binne wani Improvised Explosion Device (IED) da harshen turanci a safiyar Laraba a kan babbar hanyar Gusau zuwa Funtua a Jihar Zamfara.
Lamarin ya haifar da tsaiko na ɗan lokaci a zirga-zirgar ababen hawa.
Wakilinmu ya ruwaito cewa fashewar ta faru ne a Unguwar Chida dake ƙarƙashin ƙaramar hukumar Tsafe, yayin da babbar motar ke tafiya daga Sakkwato zuwa Kaduna.
Ana kyautata zaton ‘yan ta’adda ne suka dasa wannan na’urar, wadda ta fashe yayin da motar ke wucewa, inda fashewar ta lalata gaban tirelar baki ɗaya.
Abin al’ajabi, ba a sami asarar rayuka ba, kuma an ceto direban, Dauda Adamu, da ran sa.
Lamarin ya faru ne sa’o’i bayan da jami’an tsaro suka sake bude hanyar Kucheri zuwa Danjibga zuwa Keta, a ƙaramar hukumar Tsafe.
An rufe hanyar sama da wata guda saboda abubuwan fashewa da ake zargin ƙungiyoyin yan ta’adda sun daddasa.
Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar, Ibrahim Balarabe Maikaba, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya bayyana cewa tuni aka haɗa rundunonin ‘yan sanda da na soja, ciki har da jamian kawar da bama-bamai (EOD), don su tabbatar da lafiyar hanyar.
Matakin gaggawa da hukumomin tsaro suka ɗauka ya hana ƙarin wahala ga mazauna yankin, yayin da rufe hanyar na tsawon lokaci ya kawo cikas ga zirga-zirgar fasinjoji na tsawon sama da awanni huɗu.
