Gwamnatin Kano ta buƙaci faɗakar da jama’a kan nasarorin gwamna a manyan makarantu

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta jaddada buƙatar ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ma’aikatar yaɗa labarai da jami’an hulɗa da jama’a na manyan makarantu domin inganta isar da sahihan bayanai game da manufofi da nasarorin gwamnati ga al’umma.

Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a ofishinsa inda ya bayyana cewa taron ya mayar da hankali kan muhimman batutuwa guda biyu.

Ya ce batu na farko shi ne ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ma’aikatar yaɗa labarai da sassan hulɗa da jama’a na manyan makarantu domin tabbatar da daidaito da ingancin bayanan da ake isarwa game da manufofi da shirye-shiryen gwamnati.

Batu na biyu kuwa a cewarsa, shi ne sanar da jama’a nasarorin da aka samu ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf a ɓangaren manyan makarantu.

Waiya ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta samu gagarumar nasara wajen inganta manyan makarantu ta hanyar gyare-gyaren gine-gine, samar da sabbin dakunan karatu, inganta kayan koyarwa, horas da ma’aikata, da kuma ɗaga martabar ilimi.

Ya ƙara da cewa gwamnatin na da kudirin samar da yanayi mai kyau ga koyo da koyarwa tare da magance matsalolin da suka daɗe suna addabar manyan makarantu mallakin jihar.

Kwamishinan ya kuma buƙaci jami’an hulɗa da jama’a da su kasance masu ƙwazo da ƙwarewa wajen haskaka ayyukan gwamnati, yana mai jaddada cewa sadarwa mai inganci na da muhimmanci wajen tabbatar da cewa al’umma na samun cikakken bayani kan sauye-sauyen da ake aiwatarwa a fannin ilimi.

Ya tabbatar da cewa gwamnatin za ta ci gaba da bai wa harkar ilimi fifiko a matsayin ginshiƙi na ci gaba mai ɗorewa a Jihar Kano.

By ukarofi