Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Kimanin mutane biyar ne suka mutu sakamakon fashewar bam a kan hanyar Gusau zuwa Dansadau a jihar Zamfara.
A cewar shaidar gani da ido, Malam Yunusa Isah, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne lokacin da wasu ‘yan bindiga ɗauke da makamai suka tare babbar hanyar da misalin ƙarfe 12:00 na ranar a yau.
A cewarsa, waɗanda suka rasa rayukansu sun kasance a kan babura kuma sun taka na’urorin fashewar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutanen biyar.
Ya ce, jami’an tsaro sun riga sun mayar da martani kuma sun kori ‘yan bindigar daga wurin kafin bam din ya fashe.
A cewar sa, bam ɗin ya tashi sau uku a wasu gurare dake kan hanyar ta Dansadau bayan fashewar na farko da yayi sanadiyyar rasa rayuka biyar da suka ƙunshi maza huɗu da mace guda.
Sai dai a cewar sa fashewar ukun na daga baya, babu sahihin labarin halaka mutane a lokacin da suka fashe a yankin.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Yazid Abubakar ya tabbatar da lamarin.
Ya ce, an tura rundunar ‘yan sanda da ke yaƙi da ta’addanci zuwa yankin don yaƙi da kuma kama masu laifin a maɓoyar su.
