
Shugaba Bola Tinubu na ya tabbatar wa al’ummar Nijeriya cewa sababbin hanyoyin da ake ɗauka don magance matsalar tsaron ƙasar za su samar da nasara nan ba da jimawa ba.
Shugaban ya bayyana haka ne yayin karɓar baƙuncin Ƙungiyar Kiristoci ta ƙasa (CAN), ƙarƙashin jagorancin Shugabanta Archbishop Daniel Okoh, a gidansa da ke Legas, ranar Juma’a.
Kakakin Shugaban Ƙasa Bayo Oyanuga ne ya faɗi haka a wata sanarwa da ya fitar.
Tinubu ya bayyana cewa a shirye gwamnatinsa take wajen ƙirƙiro da ƴan sandan jihohi domin inganta tsarin tsaron ƙasar.
Ya yi kira ga CAN da ta yi aiki da gwamnatinsa domin cimma manufofin da ƙasar ke son cimmawa, inda ya ce wasu matakai da gwamnatinsa ta ɗauka na buƙatar lokaci kafin kwalliya ta biya kuɗin sabulu.
“Ƙasa na buƙatar zaman lafiya, duk da cewa wuraren da muke mulka na da faɗi. Babban kalubale ne, amma za mu yi nasara. Mun riƙe addini. Muna addu’o’i. Muna buƙatar haɗin-kai a wajenku.
“Ƴansandan al’umma da kuma na jihohi zai samu da zarar majalisar tarayya ta kammala yin duba a kan batun.
“Jiragen kai hare-hare guda huɗu da muke son saya daga Amurka za su ɗauki lokaci kafin su iso. Mun tinkari Turkiyyya ma domin neman taimako,” in ji Tinubu.
Shugaban Nijeriyar ya ce tsaiko da ake samu na shafar yadda al’umma ke kallon ƙoƙarin gwamnatinsa wajen shawo kan matsalolin tsaro, kamar yadda BBC Hausa ta wallafa.
A ƙarshe, ya ce, gwamnati na aiki tuƙuru don ganin ta mayar da zaman lafiya a ƙasar, duk da irin hare-haren sari ka-noke da ƴan bindiga da kuma ƴan tayar da ƙayar-baya ke yi a sassan ƙasar.
