Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Sanya Ido kan Gogayya Tsakanin Kamfanoni da kuma Kare Haƙƙin Masu Sayen Kayayyaki ta Nijeriya (FCCPC) ta fitar da wasu ƙa’idoji don daƙile cin zarafi, yaɗa bayanan sirri, da sauran ayyukan rashin ɗa’a daga masu bada lamuni na zamani a Nijeriya.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai zauke da sa hannun daraktan hulɗa da kamfanoni na FCCPC, Ondaje Ijagwu, wacce ta ruwaito mataimakin shugaban hukumar, Tunji Bello yana ƙaddamar da sabon tsarin a Abuja ranar Laraba.
“Da daɗewa, ’yan Nijeriya na jure cin zarafi, keta bayanain sirrin su da kuma ayyukan da ba su dace ba daga masu bada lamuni na intanet.
“Waɗannan ƙa’idoji sun shata-layi akan cewa ana maraba da manhajojin, amma ba tare da cin mutuncin mutane ba,” inji shugaban.
Bello ya ƙara da cewa, “ƙa’idojin sun bayyana matakan shari’a don hukunta waɗanda suka karya doka da kuma inganta kuɗaɗen dijital da suka dace. Babu wani mabuƙaci da ya kamata a tursasa shi, ko a ɓata masa suna, ko kuma a ƙara tsunduma shu cikin tarkon bashi da sunan bada lamuni.”
A ƙarƙashin tanadin dokar, duk masu bada lamuni na dijital dole ne su yi rajista tare da FCCPC a cikin kwanaki 90 na farawa, tare da amincewa dangane da cika ƙa’idojin bayyana gaskiya, bin bayanai, da kariyar kwastamomi.
Ma’aikatan da ba su bi ƙa’ida ba za su fuskanci hukuncin da ya kai tarar Naira Miliyan 100 ko kuma kashi 1 na kuɗaɗen da aka karɓa, da kuma yiwuwar hana kamfanin har na tsawon shekaru biyar.
